✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hukumar NCC ta kai karar mutum 7 bisa satar fasaha

Satar fasaha na hana kasa ci gaba don Najeriya na asarar akalla Naira biliyan daya kowace shekara.

Hukumar Kare Hakkin Mallaka ta Najeriya (NCC), ta shigar da karar wasu mutum bakwai a gaban kotu wadanda ake zarginsu da satar fasaha.

Darakta Janar na Hukumar NCC, Mista John Asein ne ya bayyana wa manema labarai a ranar Litinin da ta gabata a lokacin da ya kai ziyara Jihar Adamawa.

Ya ce masu satar fasahar dai sun kasance suna rubuta sunansu a rubutun da ba su suka rubuta ba wanda hakan ke bata tsarin mallaka na kasar baki daya.

Asein ya ce sun sanya hukumar bincike ne wadda ta gano inda suke kuma suka kama su.

“Wadanda ake zargi da aikata laifukan dai sun kasance mutane ne kawai wadanda muka kama da ayyukan mutane da dama tare da rubuta sunansu a kai kuma tuni mun kai su kotu.

“Satar fasaha na hana kasa ci gaba domin kasar Najeriya na yin asarar akalla Naira biliyan daya kowace shekara,” inji shi.

Shugaban NCC ya ce satar fasaha na karuwa a kullum inda wannan ayyukan da suke aikata wa ya janyo ci baya ga Najeriya.

Ya kara da cewa ’yan kasa da dama na sayan wadannan ayyukan daga wajen masu satar fasahar.

A karshe sai ya yi kira ga al’umma da su guji aikata irin wadannan ayyukan domin hukumar tana nan tana kokari wajen nemo wa tare da kama duk mai aikata irin wadannan laifukan.

%d bloggers like this: