✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar leken asiri ta kame ‘yan jarida 4 a Afghanistan

Babban laifinsu shi ne suna son su bayyana gaskiya.

Hukumar leken asiri ta Kasar Afghanistan, ta kame wasu ‘yan jaridu guda hudu bisa kai ziyara wani gari da ‘yan kungiyar Taliban ke zaune.

An zargi ‘yan jaridun da yada jita-jitar makiya a cewar masu ruwa da tsaki na Hukuamar.

‘Yan jaridun wanda ‘yan asalin kasar Afghanistan ne suna tsare a garin Kandahar da ke Afghanistan, bayan dawowar su daga wani gari mai suna Spin Boldak a ranar litinin.

Garin Spin Boldak na iyaka da kasar Pakistan wanda kungiyar Taliban ta kwace tun farkon wata Yulin da muke ciki.

Kafafen yada labarai na kasar sun yada cewa ‘yan jaridun sun je binciken wasu rahotanni da gwamnati ta yada na cewa ‘yan kungiyar Taliban sun hallaka mutane da dama a garin, zargin da ita kungiyar mai tayar da kayar baya ta musanta.

“Duk wata yada jita-jita da ke nuna goyon baya ga ‘yan ta’adda wanda kuma ya sabawa bukatun kasar Afganistan laifi ne”, a cewar mai magana da yawun Ministan Cikin Gida na kasar, Mirwais Stanikzai.

“Yanzu kusan sama da awa ashirin da hudu kenan da kame wannan yan jaridun… hakan ya saka iyalan su cikin damuwa.”

Kungiyar yan jaridu ta Afghanistan ta yi kira ga Gwamnatin kasar da ta saki wadanda aka kama da gaggawa.

“Tsare mutum ba dalili abu ne da ya sabawa ka’ida”, a cewar kungiyar ‘yan jaridun kasar.

Bayanai sun nuna cewa Afganistan ce kasa mafi hatsari ga ‘yan jaridu a duniya.

A watan Maris, wata kungiya ta ‘yan jaridun duniya mai suna ‘Watch Dog reporter’ ta ce bincike ya nuna cewa a cikin kasashe 180, Afghanista ce kasa ta 122 wadda take muzguna wa ma’aikatan jarida.

‘Yan jaridu da dama sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren da ake kai wa tunda ganin yarjejeniyar da aka cimma na janye dakarun sojoji bakin haure tsakanin kunagiyar ta Taliban da Kuma Amuruka.

Mai magana da yawun Kungiyar Taliban, Muhammad Naeem, ya ce ‘yan jaridun guda hudu sun kai ziyara garin Spin Boldak domin su binciki rade-radin cewa a kashe mutane a garin.

A cewarsa, “babban laifinsu shi ne suna son su bayyana gaskiya”.