✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Kula Da Kafafen Watsa Labarai Ta kasa ta yi barci

Kamar yadda tsarin mulki na 1992 wanda aka gyara shi a 1999 ya kafa ta, kadan daga cikin ayyukan Hukumar Kula Da Kafafen Watsa Labarai…

Kamar yadda tsarin mulki na 1992 wanda aka gyara shi a 1999 ya kafa ta, kadan daga cikin ayyukan Hukumar Kula Da Kafafen Watsa Labarai sun hada da bayar da lasisi, kulawa, tsawatarwa da kuma kula da tafiyar da kafafen watsa labarai a Najeriya. Haka kuma yana daga cikin ayyukan hukumar, ta rika ba Gwamnatin Tarayya shawara ta fuskar tafiyar da kafafen watsa labaran, musamman ma gidajen rediyo da talabijin. Wannan ya hada da amsar takardun masu bukatar kafa gidajen talabijin da rediyo, kulawa da ba da lasisin ga wadanda suka dace, ya Allah gidajen watsa labarun na gwamnati ne ko kuma na masu zaman kansu.

Tun bayan da aka shiga mulkin dimokuradiyya, an samu fantsamar kafafen watsa labarai da yawa a kasar nan. Abin takaici kuma shi ne, ba kamar yadda kafafen suka karu ba, ba a bayar da kulawa ta musamman wajen yadda ake tafiyarwa da gudanar da su kamar yadda yake a doka. Rashin bin kadin yadda ake tafiyar da kafafen, ya sanya ake samun sabani da kura-kurai wajen shirye-shiryen wasu daga cikin gidajen watsa labaran.
Abin takaicin ma shi ne, yadda wasu kafafen ke nuna goyon baya ga wasu jam’iyyun siyasa kai tsaye, musamman ta fuskar abin da ya shafi shirye-shiryen da suke gabatarwa ga al’umma. A yayin da suke neman gamsar da al’umma game da ’yan siyasar da suke mara wa baya, ta kai ga wasu kafafen watsa labarai suna surka karya da gaskiya, wani lokacin ma har kage suke domin shafa wa wasu bakin fenti.
Irin wadannan bayanai da ’yan siyasa ke yadawa game da abokan adawarsu, da ma a ce wurin yakin neman zabe ne da babu damuwa. Amma yadda ake yada kalaman gaba da nuna kiyayya ga mabiyan addinai daban-daban a kafafen watsa labarai masu lasisi, musamman ma rediyo talabijin da makamantansu, abin takaici ne da rashin dacewa; koda kuwa ma a wurin yakin neman zabe ne aka yi haka.
A wannan janibi, gidan talabijin na kasa (NTA) ya wancakalar da duk wata ka’ida ko tsarin gudanarwa, musamman ma yadda ya rika watsa shirye-shiryen ’yan jam’iyyar PDP ba tare da tacewa ba. Suna yin haka kai tsaye, ba tare da shayi ko tsoron ladabtar da su daga Hukumar Kula Da Kafafen Watsa Labarai Ta kasa ba.
Gidajen talabijin na NTA wanda na gwamnati ne da kuma AIT, wanda mai zaman kansa ne, sun rika watsa wani shirin talabijin, wanda ke kunshe da karkatattun bayanai da karerayi game da Janar Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC, inda suka rika shaci-fadi da nufin rarraba kawunan al’umma ta fuskar addini da kabilanci. Duk da cewa shirin yana dauke da abubuwan da ba su dace ba, da wadanda ba daidai ba a tarihance, amma abin takaicin mafi muni, shi ne wanda ya shafi addini da kabilanci. Wadannan gurbatattun sassa, bai kamata su wuce kuma a nuna su a gidajen talabijin din ba. Kasancewar an gabatar da su, kamata ya yi a ce hukumar NBC ta ladabtar da gidajen talabijin din, amma ba yi haka ba, an bar su salin-alin, kamar ba su aikata wani laifi ba!
Wannan ne ma ya sanya Cibiyar Kula Da Al’amuran Musulunci Ta Najeriya ta yi kira ga hukumar ta NBC cewa lallai ya kamata ta dauki tsattsauran mataki cikin gaugawa dangane da wannan gurbataccen shiri da gidajen talabijin din suka yada ga al’umma. Cibiyar ta ce, irin wadannan shirye-shirye za su iya haddasa mummunan rikicin addini a kasa.
A jawabin da ya sanya wa hannu, Babban-Sakataren cibiyar, Farfesa Ishak Oloyede ya ce abin tsoro ne da takaici a ce tashar talabijin mallakar gwamnati ce ke watsa irin wadannan shirye-shirye na batanci da tada hankali.
Irin abubuwan da suka rika afkuwa ke nan a kafafen yada labarai mallakar gwamnati kuma hukumar NBC ba ta hukunta su. Idan har ba za ta iya tsawata wa na gwamnati ba, to wane ’yanci ke gare na tsawata wa wasu masu zaman kansu? Lallai ne ya kamata hukumar NBC ta farka daga barcin da take yi, ta gudanar da bincike na yadda aka yi sakacin watsa irin wadannan shirye-shirye, wadanda suka keta dokokin gudanarwa.