✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar INEC da rarraba katin zabe na dindindin

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta sanya kanta a tsaka mai wuya lokacin da ta ce wadanda suka mallaki katin zabe na dindindin ne kawai…

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta sanya kanta a tsaka mai wuya lokacin da ta ce wadanda suka mallaki katin zabe na dindindin ne kawai suka cancanci kada kuri’a a zaben watan gobe mai zuwa.

Wannan sanarwa ta taimaka jam’iyyu su tsara harkokin ilimantar da masu jefa kuri’a kan zabe da kuma bukatar da ke akwai na magoya bayansu su yi rajista tare da karbar katin dindindin din.
Amma rahotannin da ke cewa miliyoyin wadanda suka yi rajistar har yanzu ba su karbi katin zaben na dindindin ba yana kawo takaddama da tsoron yiwuwar tauye dimbin jama’a da suka cancanta daga kada kuri’a.
Domin mallakar katin dindindin din wajibi ne kafin yin zabubbukan, abin da aka yi fata dai Hukumar INEC za ta yi duk bakin kokrinta wajen tabbatar da duk wadanda suka cancanci zaben sun samu katin.
Duka da cewa INEC a baya-bayan nan kamar makon jiya ta bada tabbacin dukkan wadanda suka yi rajistar sun samu katinsu na dindindin zuwa karshen wannan wata, har yanzu akwai tsoro ganin ranar zabe tana dada karatowa.
Kuma saboda lura da haka ne Shugaba Goodluck Jonathan da sauran fitattun ’yan Najeriya suka yi kira ga INEC ta kara zage dantse a kokarinta na tabbatar da duk wanda ya yi rajista ya samu katinsa na dindindin, kuma lura da matsayin INEC, wannan ne ‘kawai’ hanyar tabbatar da cewa ba a hana wadanda suka cancanta damarsu ta jefa kuri’a a ranar zaben ba. A kokarinta na duba wadannan koke-koke, Hukumar INEC ta sassauta wasu daga cikin tsauraran shirye-shiryenta kan rarraba katinan dindindin domin ta biya bukatar masu zabe. Misali ta sake fasalin rarraba katin zaben dindindin din daga hekdwatocin kananan hukumomi zuwa mazabun kansiloli kuma ta kara wa’adin rarraba katin daga ranar Litinin har zuwa Asabar. Hukumar a cewar Shugabanta Farfesa Attahiru Jega, ta karbi na’urorin tattara bayanai dubu 132 kuma ta rarraba dubu 25 don amfanin wuraren zabe dubu 155 a sassan kasar nan. INEC ta ce ’yan Najeriya miliyan 68 da dubu 833 da 476 ne suka yi rajista kuma suka cancanci kada kuri’a a babban zaben. Sai abin abin damuwar shi ne daga cikin wannan adadi mutum miliyan 38 da dubu 774 da 391 kawai suka karbi katin zaben na dindindin daga cikin katin zaben miliyan 54 da dubu 341 da 610 da suke hannunta. Kuma a kasa da wata daya a gudanar da zaben INEC bai kamata ta gaza ba, ganin cewa a fili yake idan ana son wasu ’yan Najeriya da suka cancanci samun katin su samu, akwai bukatar INEC ta kara zage dantse domin bayar da dama ga karin wadanda suka yi rajista su karbi katin zaben na dindindin. Tsayuwar Dakar INEC kan amfani da katin zabe na dindindin wajen zaben abu ne da ya dace kuma ya kamata a karfafa shi domin hana magudin zabe saboda a wannan mataki ba za ta yi watsi da kokarin da ta yin a tabbatar da zabe mai inganci ba tare da komawa ga amfani da katin wucin-gadi ba, wanda zai bude kofar da za a yi abubuwan da ba su dace ba. To amma domin a inganta kokarin da hukumar ke yi, wajibi ne ta tabbatar dukkan wadanda suka cancanci kada kuri’a sun samu katunan zabensu kafin zaben. Duk wani yanayi da zai sa wasu su gaza gaza yin zabe saboda kowace gazawa daga bangarenta a kauce masa. Wajibi ne INEC ta tabbatar ta yi duk abin da za ta iya wajen ganin wadanda suka cancanta sun karbi katunan zabensu ta hanyoyin da suka dace, a kara fadakar da jama’a kan amfanin karbar katunan zaben tare da tabbatar da wadanda suka cancanci jefa kuri’a ba a hana su wannan ’yanci na yin zabe ba.
Hukumar tana da ’yan makonni na ta kintsa kanta ta yadda sakamakon zaben ba ma zai kasance mai adalci kawai ba ne, har ma zai kawar da duk wani tunani kamar na tayin da Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Sambo Dasuki ya yin a cewa a dage zaben saboda ba a rarraba katin zabe ga dimbin jama’a ba.