Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS, ta gayyaci dan kasuwar nan na jihar Katsina wanda ya mallaki kamfanin Dialogue Groups Limited, Alhaji Mahadi Shehu.
Gayyatar da hukumar ta yi wa Alhaji Mahadi na zuwa ne bayan ‘yan watanni kadan da ya zargi Gwamnatin jihar Katsina da almundahanar kudin tsaro na jihar.
Hukumar ta bukaci ganin Mahadi ne tun a ranar Asabar sai dai ya yanke shawarar ba zai amsa gayyatar ba sai a yau Litinin da ta kasance ranar aiki.
Wakilinmu ya ce attajirin ya isa ofishin Hukumar DSS da misalin karfe 10.58 na safiya cikin wata bakar mota kirar Honda Civic tare da direbansa da kuma wani dan rakiya guda daya.
Mahadi wanda ya gana da manema labarai gabanin shigarsa ofishin hukumar, ya ce “sun kira ni ta wayar tarho da cewa suna bukatar gani na a ofishinsu kuma na yanke shawarar amsa gayyatar a yau Litinin da ta kasance ranar aiki.”
“Ni dai na san cewa a tsari na dimokuradiyya, kowa na da ‘yancin bayyana ra’ayinsa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada,” inji shi.