✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Alhazan Kaduna zata fara rajistar maniyyatan shekarar 2020

Shugaban Hukumar Jindadin Alhazai ta jihar Kaduna Imam Hussani Suleiman Tsoho Ikara, ‎ya bayyana cewa hukumar zata fara rajistar sunayen maniyyatan aikin hajjin badi a…

Shugaban Hukumar Jindadin Alhazai ta jihar Kaduna Imam Hussani Suleiman Tsoho Ikara, ‎ya bayyana cewa hukumar zata fara rajistar sunayen maniyyatan aikin hajjin badi a ranar 15 ga watan da muke ciki.

Imam Hussani, ya sanar da hakan ne a lokacin ganawarsa da manema labarai domin sanar da shirin fara rajistar a Kaduna.

Ya kuma bayyana cewa, za’ a fara ne a dukkanin ofisoshin hukumar da ke kananan hukumomi 23.

A cewarsa, fara yin ragistar ya biyo bayan umarnin da Hukumar kula da jindadin alhazai ta kasa NAHCON ta bayar ne na cewa, a fara yin rijistar sunayen maniyyatan da ke da sha’awar zuwa aikin hajji na shekarar 2020 don su fara ajiye kudadensu a asusun gata.

Imam Tsoho, ya ce akalla ana bukatar maniyyaci ya fara ajiye Naira dubu 800 ko kuma Naira miliyan daya da rabi kafin a bayyana kudin kujerar badi. ‎

 

‎”A  ranar 15 ga watan nan da muke ciki ne na shekarar 2019 za’a fara yin rajistar maniyatan a cibiyoyin Hukumar da ke kananan hukumomi 23 a fadin jihar.

Kuma ‎mafi karancin kudin da maniyaci zai bayar ko ajiya shine Naira dubu 800, inda kuma mafi yawan kudin ya kai Naira miliyan daya da dubu dari biyar yadda idan hukumar NAHCON ta sanar da gundarin kudin aikin, in akwai ciko da maniyyatan zasu bayar sai su cika ko kuma in akwai ragi, sai a mayar masu da sauran kudin su,” in ji shi.