An soma kaɗa ƙuri’a a Zaɓen Gwamnan Edo da ke gudana yanzu haka domin samar da magajin Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP.
Da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar wannan Asabar aka soma kaɗa ƙuri’a kamar yadda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta tabbatar.
- An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa
- Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo
Alƙaluman da INEC ta fitar sun nuna cewa mutum 2,629,025 ne suka yi rajistar zaɓe a faɗin jihar da ke da ƙananan hukumomi 18 da rumfunan zaɓe 4,519.
Sai dai masu sharhi na cewa mutanen da za su kaɗa ƙuri’ar ba za su kai haka ba la’akari da yadda aka saba gani a sauran zaɓuka.
Kazalika, ita ma INEC ta ce a cikin wannan adadi, masu kaɗa kuri’a 2,249,780 ne kaɗai suka karɓi katinsu na zaɓe.
Wannan adadi a cewar INEC, ya nuna kashi 85.57 cikin ɗari na adadin masu kaɗa ƙuri’a a yayin da mutum 379,245 ba su karɓi nasu katin zaɓen ba.
Idan aka kwatanta da zaɓen gwamna da ya gabata a jihar a shekarar 2020, daga cikin mutane 2,210,534 da suka yi rajista, 557,443 ne kawai suka fito domin tantancewa a ranar zaɓe, amma 550,242 kawai suka kaɗa ƙuri’a.
Aƙalla ’yan takara da jam’iyyun siyasa 17 ne za suke fafatawa a zaɓen da suka haɗa da maza 16 da mace ɗaya, inda manyan jam’iyyun suka kasance APC da PDP da kuma jam’iyyar Labour.