Halifan Tijjaniya kuma Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sunusi na II na wata ziyara birnin New York ta Amurka a bisa a gayyatar Majalisar Dinkin Duniya.
Majalisar ta gayyace shi ne domin halartar wani taro na musamman kan Cimma Muradun Karni SDG, a inda Halifan ya gabartar da jawabi kan ilimi.
- Tube Sarki Sunusi II: Gwamnoni ke tsoma sarakuna a siyasa – Shehu Gabam
- Kotu ta bada umarnin a saki Sanusi II
Ya kuma gana da wasu manyan mutanen aka gayyata daga sassa na duniya domin halartar taron.
Kazalika, ya yi wata ganawa ta musamman da Amina Mohammned, Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar a ofishinta
Ga yadda ziyarar ta wakana a cikin hotuna:
Aminiya ta ruwaito, a ranar Laraba Majalisar Dinkin Duniyar za ta yi taronta na shekara-shekara, karo na 77 da za a gudanar a birnin New York.