Mahajjatan bana a birnin Makka sun fara tsayuwa a filin Arfa, wacce take babbar jigo a cikin ibadar aikin Hajji.
Ranar Arfa ita ce rana mafi girma da muhimmnanci a duka kwanakin aikin hajji. Ko a hadisi ma ya zo, Annabi SAW ya ce Arfa ita ce hajji.
Ga kaɗan daga cikin yadda alhazan suka fara gudanar da wannan ibada mai muhimmanci inda ake sa ran za su yini suna ibada daban-daban.