✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda Kano ta yi cikar ƙwari yayin ziyarar Ganduje

Ganduje ya kai ziyarar ne domin jajanta wa waɗanda hatsarin mota ya rutsa da su a jihar.

Ɗaruruwan mutane a ƙaramar hukumar Bichi ta Jihar Kano, sun yi dafifi a ranar Asabar domin tarbar Shugaban Jami’yyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Ganduje, ya je Bichi ne domin jajanta wa waɗanda hatsarin mota ya rutsa da su, da iyalan ’yan sandan da suka rasa rayukansu a hatsarin.

’Yan sandan sun yi hatsari ne yayin da suke dawo daga zaɓen Gwamnan Jihar Edo da aka gudanar makon da ya gabata.

A farkon makon nan ne, Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) a Jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar ’yan sanda biyar sakamakon hatsarin.

Hatsarin ya faru ne a kan hanyar Zaria zuwa Kano, kusa da garin Ƙarfi.

Ga hotunan ziyarar Ganduje a ƙasa: