✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda aka yi sulhu da ƙasurgumin ɗan fashin daji Ado Aliero a Katsina

An zauna da Ado Aliero da Kamilu Buzaru da Dogo Nahali da Wada Jargaba da Dahiru Buzu haka ma da Nagoggo.

Wasu mazauna Jihar Katsina sun yi zaman sulhu da wasu shugabannin ’yan daban daji da suka addabe su.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an yi taron sasanci da ’yan bindigar daji ne a Ƙaramar Hukumar Danmusa, wanda rundunar sojoji ke shiryawa, inda Adamu Aliero ya jagoranci sashen ’yan bindigar.

BBC ya ruwaito Kwamishinan Tsaro da Harkokin Ciki Gida na Katsina na cewa al’ummar garin Bicci da ke yankin Ƙaramar Hukumar Danmusa sun zauna tare da Ado Aliero da sauran wasu shugabannin ’yan bindigar aƙalla goma.

“An zauna da Ado Aliero da Kamilu Buzaru da Dogo Nahali da Wada Jargaba da Dahiru Buzu haka ma da Nagoggo,” in ji shi.

Hotuna daga Ahmed Kabiru S/Kuka