✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar surukar Ganduje a Kano

An yi jana'izarta gidan Ganduje da ke Kano.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje da wasu jiga-jigan jami’yyar a Jihar Kano, sun halarci jana’izar surukarsa wadda ta rasu a ranar Litinin.

Limamin gidan Ganduje, Malam Auwal Khalid ne ya jagoranci jana’izar surukar tsohon gwamnan na Kano.

Aminiya ta ruwaito cewar surukar tsohon gwamnan Hajiya Asiya Gauyama, wadda mahaifiya ce ga matarasa Hafsat Abdullahi Ganduje, ta rasu a ranar Litinin.

Babban sakataren yaɗa labaran Ganduje, Edwin Olofu ne, ya sanar da rasuwarta a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin.

Ga hotunan yadda jana’izar ta kasance: