Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya sauka a ƙasar Sweden, inda ya kai ziyarar aiki na kwana biyu domin ƙara ƙulla a tsakanin ƙasashen.
A yayin ziyarar, Shettima zai tattauna da Firaminista da manyan jami’an gwamnatin Sweden domin ƙara ƙulla dangantakar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
Zai kuma gana da Gimbiya mai jiran gado, Victoria a yayin ziyarar, wadda ya samu rakiyar Gwamnan Filato Caleb Mutfwang da Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar da wasu manyan jami’an gwamnatin Nijeriya.