Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL), ya fara hako mai a rijiyar Ebenyi da ke Jihar Nasarawa.
Babban jami’in kamfanin NNPC, Mele Kyari, a lokacin da yake magana a ranar Talata a rijiyar Ebenyi-A da ke unguwar Ajibu da ke Karamar Hukumar Obi ta jihar Nasarawa.
Ya ce NNPC na bakin kokarinsa wajen kara samar da yawan man da ake hakowa a kullum daga ganga miliyan 1.6 kowace rana zuwa ganga miliyan uku a rana.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya halarci bikin fara hako man, ya ce “Yau ne aka fara aikin hako mai a Benuwai. Wannan ya yi dai-dai da sinadarin yankin Kolmani na babban titin Benuwai.”
Ga wasu daga cikin hotunan yadda aka fara hako man: