✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Masaukin Ronaldo da budurwarsa a Saudiyya

Ronaldo da budurwarsa sun kama dakuna 17 a otel din da suka kama hawa biyu

Cristiano Ronaldo, sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr da ke Saudiyya da budurwarsa sun tare a wani otel na alfarma da suke biyan kudin dakuna Yuro miliyan 3.04, kimanin Naira biliyan 1.5, a shekara.

Kudin dakunan da masoyan suka kama a birnin Riyadh ya kai Naira miliyan 122.6 a wata, wato Naira miliyan hudu a kullum.

Duk da Saudiyya ta haramta tarewar budurwa da saurayi, Ronaldo da masoyiyarsa, Georgiana Rodriguez, sun kama dakuna 17 a otel din da suka kama hawa biyu.

Rahotanni sun nuna an yi wa dan wasan da masoyiyarsa sassauci kuma za su rika zama ne tare da ’ya’yansu biyar a otel din, kafin su koma katafaren gidansu na Yuro miliyan 12, kwatankwacin Naira biliyan 5.9.

Ga wasu daga cikin hotunan.