✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shahararriyar ’yar kwallon kafa ta ziyarci Gwamnan Legas

Gwmanan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya karbi bakuncin kwararriyar ’yar wasan kwallon kafa ’yar Nigeriya da ke taka leda a kungiyar Barcelona, Asisat Oshoala. Gwamna…

Gwmanan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya karbi bakuncin kwararriyar ’yar wasan kwallon kafa ’yar Nigeriya da ke taka leda a kungiyar Barcelona, Asisat Oshoala.

Gwamna Sanwo-Olu ya karbi bakuncin Asisat ne a gidan gwamnatin jihar da ke Marina inda ya bayyana ta a matsayin jakadiya ta gari.

“Jakadiyar jihar Legas ce da ta fito daga yankin Ikorodu. Mun buga kwallo da ita a lokacin da ta kawo min ziyara; tabbas ni ma har yanzu da kwarewata”, inji shi.

Sanwo-Olu ya ce Asisat Oshoala ta yi masa bayanin shirye-shiryenta a bangaren gidauniyarta kuma a shirye yake ya ba da gudumawarsa.

Gwamna Sanwo-Olu yayin murza tamaula da Asisat
Gwamna Sanwo-Olu yayin da Asisat ke sanya hannu a jin wani kwallo.
Gwamna Sanwo Olu tare da Asisat a Gidan Gwamnatin Jihar Legas.
Gwamna Sanwo-Olu yayin da yake nuna wa Asisat kwarewarsa a kwallon kafa.
Asisat na kallon yadda Gwamna Sanwo-Olu ke murza leda.
Gwamna Sanwo Olu yayin da yake nuna wa Asisat kwarewarsa a kwallo
Gwamna Sanwo-Olu yayin da yake nuna wa Asisat kwarewarsa a kwallon kafa.
Asisat da Gwamna Sanwo-Olu suna taka leda tare a fadar gwamnan.