✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hotuna: Gwamna Kirista ya gina Babban Masallacin Juma’a da kudinsa a Ibadan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero sun halarci bikin bude Masallacin Adogba da ke birnin Ibadan, wanda Gwamna…

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero sun halarci bikin bude Masallacin Adogba da ke birnin Ibadan, wanda Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya sake ginawa da kudin aljihunsa.

Gwamnan, wanda ba Musulmi ba ne, ya dauki nauyi sake gina masallacin ne bayan an rusa shi a shekarar 2020 a dalilin aikin gina wata tashar mota a babbar hanyar Iwo-Road a Ibadan.

Sabon masallacin da gwamnan ya cika alkawarin ginawa bayan an canza masu matsuguni zuwa inda yake a yanzu, ya hada da makarantun Islamiya da na boko da dakunan karatu da bincike na zamani a harabarsa.

Ga yadda bikin ya gudan cikin hotuna:

Sarakin Musulmi da Sarkin Kano da kuma Babban Limamin Ibadan yayin da ake gabatar da jawabai a taron. (Hoto: IKrimatu Suleiman)
Wasu daga cikin hadiman Sarkin Kano a bikin bude masallacin na Ibadan. (Hoto: IKrimatu Suleiman)
Gwamna Seyi Makinde yana yi wa Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero maraba a masallacin. (Hoto: IKrimatu Suleiman)
Gwamna Seyi Makinde da Sarkin Kano na yi wa Sarkin Musulmi maraba a wurin bikin bude masallacin (Hoto: IKrimatu Suleiman)
Gwamna Seyi Makinde yana zagayawa da Srkin Muslmi da kuma Sarkin Kano cikin Masallacin domin ganewa idonsu. (Hoto: IKrimatu Suleiman
Gwamna Makinde da Sarkin Musulmi a bikin. (Hoto: IKrimatu Suleiman)
Sarkin Musulmi yayin da ya ke bude masallacin Gwamnan jihar Seyi Makinde da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran manyan baki na taimaka masa. (Hoto: IKrimatu Suleiman).