HOTUNA: Bikin bude taron horaswa na Gidauniyar Kannywood
Gidauniyar Kannywood ta shirya taron kara wa juna sani ga ’yan masana’antar shirya fina-finai tare da tallafin Gwamnatin Jihar Kano. An yi bikin bude taron…
DagaYakubu Liman
Mon, 3 Oct 2022 11:42:13 GMT+0100
Gidauniyar Kannywood ta shirya taron kara wa juna sani ga ’yan masana’antar shirya fina-finai tare da tallafin Gwamnatin Jihar Kano.
An yi bikin bude taron na kwana biyar a ranar Lahadi wanda ya samu halarcin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Barau Jibrin da manyan jami’an gwamnatin jihar, da kuma ’ya’yan masana’antar shirya fina-finan daga ciki da kuma wajen Jihar Kano.
Gwamnan ya kuma shirya wa ’yan Kannywood liyafar cin abincin dare a Fadar Gwamnatin da ke Karamar Nasarawa.
Ga wasu hotunan yadda bukuwan suka wakana:
Shugaban Gidauniyar Kannywood Shu’aibu Yawale da Gwamnan Kano Umar Ganduje, da kuma Sanata Barau Jibrin, a taron (HOTO: Shu’aibu Yawale)Gwamna Ganduje na gabatar da jawabinsa a bikin bude taron (HOTO: Khalid Musa)Farfesa Abdallah Uba Adamu na gabatar da jawabinsa a lokacin taron (HOTO: Khalid Musa)
Isa Bello Ja tare da wasu daga cikin mahalarta taron (HOTO: Khalid Musa)Wasu daga cikin mahalarta taron mata ‘yan fim (HOTO: Khalid Musa)TY Sha’abana tare da wasu mahalarta taron a yayin bikin (HOTO: Khalid Musa)Jamila Gamdare da Mansura Isah a yayina taron (HOTO: Khalid Musa)Wasu jarumai mata a yayin taron (HOTO: Khalid Musa)Dandazon jama’ar da ta taru a wajen bikin bude taron bitar (HOTO: Khalid Musa)A.A Zaura da Shugaban Gidauniyar Kannywood Foundation Shu’aibu Yawale, da Gwamnan Kano Ganduje, da Sanata Barau Jibrin, da kuma Kwamishinan yada labarai Mohammed Garba bayan kammala taron (HOTO: Shu’aibu Yawale)Sani Mu’azu da kuma wasu daga cikin jami’in Kannywood Foundation a liyafar gidan gwamnati (HOTO: Kannywood Foundation)Wasu daga cikin jaruman a teburin cin abinci a walimar da gwamna ya shiryawa a giadan gwamanati (HOTO: Kannywood Foundation)Abdullahi Zakari Ligidi da Yakubu Ibrahim da kuma wasu daga cikin dattawan Kannywood a taron liyafar (HOTO: Kannywood Foundation)Adamu Kwabon Masoyi da Rufa’i Shehu Minjibir a bikin liyafar (HOTO: Kannywood Foundation)Shehu Hassan Kano da Aliyu Sambo a taron walimar (HOTO: Kannywood Foundation)Shugaban Kannywood Foundation Shu’aibu Yawale na jawabin maraba a taron liyafar (HOTO: Kannywood Foundation)Jaruma Rahama MK a taron liyafar (HOTO: Kannywood Foundation)Wasu jarumaia mata a taron liyafar a gidana gwamnati (HOTO: Kannywood Foundation)Dan Auta da Baba Ari a taron liyafar (HOTO: Kannywood Foundation)Shugaban kungiyar dattawan ‘yan fim Auwalu Isma’il Mashal da sauran dattawan ‘yana fim a taron (HOTO: Kannywood Foundation)Zahra’u Mohammed Adama da Lubabatu Madaki a taron liyafar (HOTO: Kannywood Foundation)Asma’u Sani da Hadiza Mohammed da kuma Fati shehu a wurin taron liyafar (HOTO: Kannywood Foundation)