Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da wasu ayyukan ci gaba da ya yi a Kauyen Dorawa da ke Jihar Nasarawa.
A ranar Asabar ce Kwankwaso ya bude ginin makarantar firamare da injinan tiransifoma na wutar lantarki, da kuma rijiyar burtsatse da ya gina a kauyen na Dorawa da ke Karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa, mai makwabta da Abuja.
- Yadda ta kwashe tsakanina da ‘aljana’ Ummulhairi (4)
- Ambaliyar Ruwa: Peter Obi ya raba burodi 24 a matsayin tallafi
Amintacciya ta ruwaito cewa, kauyen ya shafe shekaru 30 babu makaranta, kuma shekaru 3 babu wutar lantarki.
A makarantar da ya gina, ya sa kayan aiki, sannan ya kuma dauki nauyin malamai 10 da za su koyar da dalibai.
Ga yadda bikin bude ayyukan ya gudana a cikin hotuna: