An fara jigilar fasinjoji bayan bude filin jiragen sama na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano a safiyar Asabar 11 ga Yuli, bayan kusan wata uku da rufe sufurin jirage na cikin gida a Najeriya.
Annobar COVID-19 ce ta tilasta rufe bangaren wanda aka sake budewa a ranar 8 ga watan Yuli, da filayen jirage na Legas da Abuja, bayan sanya matakan kariya da kuma bayar da tazara a dukkanin matakai.
Ga wasu hotunan yadda harkoki suka fara gudana a filin jirgin:
Ana auna zafin jikin wani matafiyi kafin ya shiga cikin ginin filin jirgin Malam Aminu Kano. Wani fasinja a lokacin da ake yi wa jakarsa feshin magani a filin jirgin. Kayan wasu fasinjoji da suka sauka a filin jirgin. Ma’aikatan Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Sama na lura da yadda ake tafiyar da fasinjoji. Wani jimi’in hukumar shige da wasu matafiya suna bin layi tare da bayar da tazara. Yadda ake bayar da tazara a wurin tantance fasinjoji. Ana bayar da tazara tsakanin fasinjojin da suka sauka a filin jirgin.