✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hoton madubi

Wata Bafulatana ce ta je birni wajen ’yan uwanta, to gidan da suke akwai irin madubin jikin bango a kofar bandaki. To duk lokacin da…

Wata Bafulatana ce ta je birni wajen ’yan uwanta, to gidan da suke akwai irin madubin jikin bango a kofar bandaki. To duk lokacin da ta zo shiga bandaki sai ta rika ganin hotonta amma ba ta san cewa ita ce ba. Ka san Fulani da kunya, ba ta yadda su hada ido da hoton, sai ta wuce ta ce: “Ina wuni?” Kullum haka, sai rannan ta ce wa matar gidan: “Ni kam waccan matar kullum idan na gaishe ta ba ta amsawa.” Sai ta ce mata wace ce haka? Sai suka tafi don ta ga ko wace ce. Koda suka isa wurin sai ta ga madubin kofar bandaki ne.
Daga Muhammad Nasir Muhammad, 08033995650