✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hodgson ya yi murabus daga horar da Ingila

Manajan kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila, Roy Hodgson ya yi murabus daga horar da kungiyar bayan da kasarsa ta sha kashi a hannun kasar…

Manajan kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila, Roy Hodgson ya yi murabus daga horar da kungiyar bayan da kasarsa ta sha kashi a hannun kasar Iceland a zagaye na biyu na gasar cin Kofin Nahiyar Turai da ake gudanarwa a kasar Faransa.
Manajan mai shekara 68 ya horar da kungiyar na tsawon shekara hudu bayan yam aye gurbin dan kasar Italiyan nan Fabio Capello, kuma ya samu nasarar lashe uku daga cikin manyan wasanni 11 a wasan karshe da ya jagoranta.
kasar Iceland mai yawan jama’a dubu 330 kacal tana daya daga cikin kungiyoyin da ake ganin ba za su taka abin a zo a gani ba a gasar, inda kuma take matsayi na 34 a duniya.
“Ina bakin ciki zan kawo karshen aikina ta wannan hanya, amma wadannan abubuwa sun riga sun faru,” inji Hodgson.