✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hizba ta kama matashin da ke kokarin sayar da kansa a Kano

Hisbah ta ce ta kama shi ne saboda abin da yake kokarin yi ya saba da Musulunci.

Hukumar Hizba a Jihar Kano ta kama matashin nan dan asalin Jihar Kaduna da ya zo Kano don sayar da kansa kan kudi Naira Miliyan 20.

Matashin, mai suna Aliyu Na Idris wanda aka fi sani da Abba Daru, mai shekara 26 ya yi tallan kansa a makon jiya a Kano inda ya ce zai sayar da kan sa ne saboda rashin kudin da yake fama da shi.

Tun da farko dai matashin, wanda ya fito daga Karamar Hukumar Soba ta Jihar Kaduna, a cikin wani faifan bidiyo da ya karade shafin sada zumunta na Facebook, ya ce ya janye yunkurin nasa bayan da ya gano hakan haramun ne a Musulunci.

Shugaban hukumar ta Hisbah, Dokta Haruna Ibn Sina  ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce hakan haramun ne a Musulunce.

Ibn Sina ya ce, “Mun kama shi ranar Talata kuma ya kwana a hannunmu saboda abin da ya akaita haramun ne a addinin Musulinci, ba ka da damar sayar da kanka a kowanne hali ka tsinci kanka.

“Mun shaida masa cewas a matsayinsa na dan Adam, ba shi ya mallaki kansa ba, saboda haka kuma ba shi da yancin sayar da kansa.

“Ya kuma ji wa’azin da muka yi masa, sannan ya janye kudurin nasa,” inji Ibn Sina.

Daga nan Kwamandan ya yi kira ga jama’a, musamman ma iyaye da su kula da tarbiyyar ’ya’yansu kamar yadda Allah Ya dora musu don ci gaban al’umma.

Sai dai a wani faifan bidiyon na daban, matsahin ya ce yana nan kan bakarsa matukar bai samu ganin Naziru Sarkin waka ba kuma kofa a bude take ga duk mai sayen sa.