Hukumar Hisbah a Jihar Jigawa ta ce mayar da mutum 681 da suka bace ga iyalansu a shekarar 2021.
Babban Kwamandan hukumar a Jihar, Ibrahim Dahiru ne, ya shaida hakan ga Kamfanin Dillacin Labarai (NAN), a Dutse a ranar Talata.
- Cristiano Ronaldo ya samu kyautar FIFA ta musamman
- ’Yan bindiga sun sace Hedmasta a Neja, sun bukaci a basu N100m
Kwamandan ya ce daga cikinsu akwai almajirai 372 da mata 237 wanda suka bar gidajen iyayensu saboda auren dole.
“Akwai masu tabin hankali guda 37, sai mutum 31 da suka bace da kuma kananan yara hudu da aka aika su aikatau,” a cewarsa.
Kazalika, Kwamandan ya ce hukumar ta yi nasarar tallafa wa mutum 548 a Jihar, da ke da bukata ta musamman.
Dahiru ya ce hukumar ta gudanar da taron wayar da kai ga mutum 1,683 a Kananan Hukumomi 27 da ke fadin Jihar ta Jigawa.
Har wa yau, Kwamandan ya jinjina wa yadda jama’ar Jihar ke basu hadin kai da taimako wajen gudanar da aikinsu wajen yakar munanan dabi’u.