✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta kwace daruruwan kwalaben giya a Jigawa

An giyan ne a samamen da Hisbah ta kai ga garin Gujungu.

Hukumar Hisbah a jihar Jigawa, ta kwace daruruwan kwalaben giya a samamen da ta kai wani otal da ke jihar.

An kai sumamen a daren ranar Juma’a a garin Gumel, kamar yadda Kwamandan Hukumar, Ibrahim Dahiru, ya bayyana.

“Jami’anmu sun kai samame wani otal da ke garin Gujungu a Gumel, kuma an yi nasarar kame kwalaben giya 308.

“Sai dai ba mu cafke kowa daga cikin wanda suke ta’ammali da giyar ba, wanda suka ara ana kare tun bayan da suka hangi jami’anmu.

“Zan yi amfani da wannan dama don tunatar da jama’a cewa, sha ko ta’ammali da giya ya haramta a fadin Jihar Jigawa, kuma Hisbah za ta ci gaba da yaki da shan ta,” a cewar Dahiru.

Sannan ya kara da cewa sun damka giyar ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar, don ci gaba da bincike.

Dahiru, ya jadadda cewa za su ci gaba da yaki da duk wani mai kokarin kawo munanan dabi’u a Jihar ta Jigawa.