✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hisbah ta kama mutum 6 da kwalaben giya 500 a Jigawa

Akwai mata a cikin mutanen da ’yan Hisbah suka ritsa da dare a wata mashaya.

Hukumar Hisbah a Jihar Jigawa ta kame mutum shida ciki har da mata uku a wata mashaya bisa zargin ta’ammali da barasa.

Hisbah ta kuma kwace kwalaben giya kimanin 500 yayin samamen da ta kai gidan barasar da ke Birnin Kudu.

Kwamandan Hukumar a Jihar Jigawa, Ibrahim Dahiru, ya ce tuni hukumar tuni ta mika barasar ga hukumar ’yan sandan jihar.

Kwamandan ya ce an kame mutanen ne lokacin da askarawan Hisbah suka kai samame kan mashayar da misalin karfe 9 na daren Litinin.

Ya ce shan barasa ko miyagun kwayoyi haramun ne a duk fadin Jihar Jigawa.