✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisba ta sa zare da masu sayar da giya a Jigawa

Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa ta kafa kwamitin da zai yi yaki da badala da nufin kawar da ayyukan assha a fadin jihar, inda Kwamandan…

Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa ta kafa kwamitin da zai yi yaki da badala da nufin kawar da ayyukan assha a fadin jihar, inda Kwamandan Hukumar Hisba ya kaddamar da kwamati a karkashin kwamanda mai kula da Karamar Hukumar Birnin Kudu, Malam Yunusa Barau.

Jim kadan da kafa kwamitin, Malam Barau ya zauna da masu sayar da giya da gidajen karuwai da nufin sanar da su ka’idoji da dokokin da suka shafi harkokinsu.

A yayin zama da kungiyar masu sayar da giyar a yankin Birnin Kudu da Gwaram da Dutse sun nuna damuwarsu kan matakin da gwamnati ta dauka na kokarin hana su kasuwancinsu na sayar da giya da karuwanci a jihar.

Mai magana da yawun kungiyar, Mista Etibate ya bayyana wa Hisba cewa ya zo Jihar Jigawa tun kimanin shekara 40 da suka gabata, kuma shi bai iya komai ba sai sayar da giya, saboda haka ya bukaci Gwamnatin Jigawa ta sayi gidan da inda yake zaune a Unguwar Gangare da ke garin Birnin Kudu saboda ya samu jarin da zai sauya sana’a ya rabu da sayar da giyar.

Ya roki Hukumar Hisba ta daga masu kafa saboda a cewarsa wadansu da dama sun dauko bashin giyar ce daga Jihar Bauchi yayin da wadansu kuma sun sayo ne da kudinsu amma aka kwace ta, a yanzu an karya su ba su da komai.

Ya ce akwai bukatar Hisba ta daga wa kabilar Ibo kafa wajen saye da sayar da giya da kuma shanta, saboda ita giya tamkar wani sashi ne na rayuwar Ibo.

Shi kuma Mista Achuegbo A.I a jawabinsa, nema ya yi Hukumar Hisba ta taimaka wa ’ya’yan kungiyar ta Ibo mazauna Jigawa masu harkar gidajen giya da wata hanyar da za su sauya sana’a wadda za su iya dogaro da kansu bayan sun daina sayar da giyar.

Da yake mayar da jawabi, shugaban kwamitin ya hore su da su gaggauta samun sana’ar yi, amma ban da batun sayar da giya da kwayoyi masu sa maye. Ya ce yin hakan ya saba wa dokokin da Majalissar Dokokin Jihar Jigawa ta shimfida, kuma duk wanda ya yi kunnen kashi wajen kin bai wa dokar hadin kai, to doka za ta yi aiki a kansa.

Ya ce sun kira taron ne saboda su fadakar da duk masu sayar da giya a jihar game da dokar, sannan a nan gaba ya ce za su zauna da masu sayar da miyagun kwayoyi, da dillalan tabar wiwi da sauran masu miyagun sana’o’in da ke cutar da al’umma, kuma da zarar sun kammala fadakar da wadanda abin ya shafa za su fara gudanar da ayyukansu gadan-gadan.