A wani abu mai kama da al’mara, kasar Saudiyya ta doke Ajantina da ci 2-1 a wasansu na farko na Gasar Cin Kofin Duniya a kasar Qatar.
Lamarin ya zo wa masu kallon kwallon kafa da ba-zata domin ana kallon Saudiyyar a matsayin kasa mai raba maki a gasar, musamman ganin da Ajantina za ta buga, kasar da ake sa ran za ta iya lashe gasar.
- Ronaldo ya raba gari da Manchester United
- Qatar 2022: Saudiyya ta lallasa Argentina a Gasar Cin Kofin Duniya
Sai dai wadanda suka san kocin Saudiyya na yanzu, ba su yi mamaki ba, domin an san shi da kokarin canja salon kwallo a duk kasa ko kungiya da ya horar.
Hervé Jean-Marie Roger Renard dan asalin kasar Faransa ne da ya horar da kasashen Zambia da Ivory Coast da Moroko da kungiyoyi irinsu Lille, Cambridge United da sauransu.
Ya jagoranci kasar Zambia ta lashe Gasar Cin Kofin Afirka ta shekarar 2012, sannan ya jagoranci kasar Ivory Coast ta lashe gasar ta shekarar 2015.
Yanzu haka shi kadai ne koci da ya jagoranci kasashe biyu suka lashe Gasar Cin Kofin Afirka.
Sai dai kafin ya fara samun nasara a horar da ’yan wasa, haifaffen yankin Aix-les-Bains na kasar Faransa, ya buga kwallo a kungiyoyin AS Canned da Stade de Vallauris da SC Draguignan tsakanin shekarar 1983 zuwa shekarar 1998.
Ya yi ritaya daga taka leda bayan ta ki karbarsa, sai ya koma mai share-share a kungiyar SC Draguignan, har ya kai ga bude nasa kamfanin share-sharen.
A shekarar 1999 ce SC Draguignan ta dauke shi mai horarwa, sannan a shekarar 2001 ya zama mataimakin mai horar da ’yan wasan kungiyar Shanghai Cosco ta China.
Daga nan ne ya fara samun daukaka kadan-kadan har zuwa yanzu.
Yanzu haka kasar Saudiyya ta fara Gasar Cin Kofin Duniya ta bana da kafar dama, sai dai ko za ta yi nisa, ko ba za ta yi ba, wannan sai lokaci ne zai nuna.