✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hausawan Takum sun koka kan kisan mutane 32

Al’ummar Hausawan ƙaramar hukumar Takum da ke jihar Taraba na neman gwamnati ta hukunta ƴan ƙabilar Kuteb da suke zargin sun kashe musu mutane 32.…

Al’ummar Hausawan ƙaramar hukumar Takum da ke jihar Taraba na neman gwamnati ta hukunta ƴan ƙabilar Kuteb da suke zargin sun kashe musu mutane 32.

Sai dai al’ummar Kuteb sun musanta wannan zargin.

Kakakin al’ummar, Alhaji Sani Abdullahi Tullu ne ya bayyana wannan buƙata a jawabin da ya yi ƴan jarida a birnin Jalingo ranar Lahadi.

Hausawa sun zargi ’yan kabilar Kutep da kashe musu mutane a kauyen Taraba

Mutum 16 sun mutu a rikicin kabilanci a Taraba —’Yan sanda

Alhaji Tullu ya  nemai gwamnantin jihar Taraba ta yi binciken ƙwaƙwaf kan abin da ya kira ‘kisan gillar da ake yi wa Hausawa’.

Ya kuma buƙaci gwamnatin ta tabbatar ta hukunta waɗanda aka samu da laifi.

Ya ƙara da cewa “Al’ummar Hausawa sun fi shekara 200 su na zaune lafiya da maƙwabtansu Jukun, Chamba, Ichen, Kuteb da Tiv a Takum.

“Sai dai a ƴan shekarun nan al’ummar Hausawan Takum na fama da hare-hare daga ƙabilar Kuteb ba tare da wani dalili ba.”

Ya ce matasan Kuteb na kashe Hausawa ne sakamakon rikicin da ke tsakaninsu da Fulani makiyaya.

Alhaji Tullu ya kuma yi zargin cewa daga 11 ga Mayun 2022 babu wani wata da ya wuce ba tare da matasan Kuteb sun kai farmaki kan Hausawa ba.

Amma a martaninsa, shugaban ƙungiyar Kuteb na ƙasa, Mr Emmanuel Ukwen ya musanta wannan zargin.

Ya kuma zargi Hausawan Takum da bayar da mafaka ga Fulanin da ke kai hari kan Kuteb.

Mr Ukwen ya kuma ce ya gana da wakilan al’ummar Hausawa domin sulhunta tsakanin ƙabilun biyu.