Aminiya ta tattauna da wakilin Sashen Hausa Na Rediyon kasar Sin a Najeriya, Chun Weiwei, wanda aka fi sani da sunan Malam Murtala. Ya samu digiri har biyu a fannin Hausa. A cikin shekara hudu kacal ya koyi Hausa a kasar China, amma ya iya magana da rubutu da harshen kamar jakin Kano.
Bari mu fara da tarihinka a takaice.
Assalamu alaikum, sunana Malam Murtala da Hausa, amma da Sinanci sunana Chun Weiwei kuma an haife ni a 1986, cikin watan Maris, a wani gari mai suna Birnin Nianjing da ke gabashin kasar Sin, wato China ke nan. Na girma a can, na yi makarantar firamare da kuma sakandare. Sa’annan, bayan da na kammala makarantar sakandare, ka san a wancan lokaci ina sha’awar koyon harshe, dayake da ma na iya harshen Ingilishi sosai, lokacin da nake makarantar sakandare. A haka aka ce za a ba ni dama in zauna jarabawar neman shiga jami’ar koyon harsunan waje ta Beijing. (Beijing Forign Studies Unibersity), wadda ta yi fice a kasarmu wajen koyar da harsunan kasashen waje. Allah Ya ba ni sa’a na ci wannan jarabawa, na shiga wannan jami’a a 2008 kuma fannin karatuna shi ne harshen Hausa saboda ka san mu a wannan jami’a, muna da harsunan kasashen waje guda sittin da wani abu, ciki har da harsunan Afirka guda biyu; na Hausa daga Yammacin Afirka da kuma Swahili daga Gabashin Afirka. Shi ne na koyi Hausa, tun daga 2008 zuwa 2012. Wato shekaru hudu na yi ke nan ina koyon wannan yare na Hausa a kasar Sin.
A wancan lokaci muna da malamai guda hudu amma daya ne kacal daga cikinsu da ya kasance Bahaushe, sunansa Malam Balarabe Shehu Illela. Na san mutane da yawa sun san shi, har yanzu yana can kasar Sin yana harkokinsa. Sauran ukun, wato Malam Yusufu da Malam Shekarau da Malama Suwaiba, dukkansu sun yi karatun Hausa a Jami’o’in A.B.U. da B.U.K. wato a Zariya da kuma Kano. Su suka koya mini Hausa kuma suka lakaba mini sunan Hausa, wato Murtala.
Wato ke nan dukkan karatunka a can kasar Sin ka yi shi?
E, a wancan lokaci, daga 2008 zuwa 2012, ban taba zuwa Nahiyar Afirka ba, sai dai kawai na yi karatuna a China.
To, mene ne matsayin karatun naka ya zuwa yanzu a fannin Hausa?
Ina da digiri na farko da kuma digiri na biyu a kan harshen Hausa kuma duk a can kasar Sin na yi karatuna.
Malam Murtala, me ya ba ka sha’awa kuma ya ja ra’ayinka ka ga cewa ya dace ka yi nazarin harshen Hausa?
Ka san kafin 2008, ban taba jin sunan yaren Hausa ba. Na dai taba jin sunan Najeriya, amma ban taba jin na Hausa ba kafin lokacin. Mene ne Hausa? Na duba intanet, wato Yanar gizo ke nan da Hausa. Na yi ta bincike-bincike, inda na gano cewa Hausa wata kabila ce ko kuma wata al’umma ce a Yammacin Afirka, ba ma kawai a Najeriya ba. Na yi bincike na tarihin Hausawa da al’adun gargajiya na Hausawa, sannan na yi bincike kan al’ummomin Najeriya baki daya. Na gano cewa Nahiyar Afirka cike take da abubuwan mamaki, masu ban al’ajabi. Wannan shi ne ya ba ni karfin gwiwa, wajen koyon wannan harshe na Hausa. Tun a lokacin na kudurci cewa, in Allah Ya yarda, wata rana zan je Najeriya saboda ku Hausawa kukan ce gani ya kori ji kuma ilimi a kafa yake. Wannan shi ne dalilin da ya sanya na yi sha’awar koyon wannan harshe.
Bayan na kammala karatuna a 2012, na samu aiki a matsayin wani dan jarida a Sashen Hausa Na Gidan Rediyon kasar Sin (Hausa Serbice of China Radio International).
Kafin ka zo nan Najeriya, wadanne irin shirye-shirye ka rika gabatarwa a wannan gidan rediyo a can China?
Kafin zuwana Najeriya, a can kasar Sin na rika karanta labarai da dumi-duminsu, kamar nakan ce: ‘Masu sauraro, barkan ku da war haka, Sashen Hausa Na Rediyon kasar Sin ke magana har yanzu, ku kasance da Murtala; a ji kanun labaru kamar haka…’ Wannan shi ne ta bangaren labarai. Bayan haka kuma na dauki shirye-shirye guda biyu: Na farko, ana kiran shi ‘Allah daya Gari Bamban,’ inda muke maida hankali a kan wasu al’adun kasar Sin. Mukan kwatanta al’adun kasar Sin da na Hausawa ko kuma al’adu na Afirka, shi Allah daya amma gari bamban ke nan. dayan kuma, shiri ne a kan kade-kade da wake-wake daga kasashen Afirka, inda muke maida hankali a kan wakoki ko kuma kade-kaden Hausa ko na Najeriya baki daya. Kamar nakan saka wakokin marigayi Mamman Shata ko na Fati Nijar da sauransu kuma nakan maida hankali ga wakokin Kudancin Najeriya, kamar su P-Skuare (Peter da Paul) da kuma Tuface Idibia. Amma da na zo nan, ka san a nan ni kadai ne wakilinsu, shi ya sanya abubuwan da nakan dauko, ko kuma in ce intabiyu shi ne kamar idan na je wasu wurare na yi hira da mutane idan wani abu ya faru. Kamar ko wani hari idan ya faru ko wani biki ne da za a yi, da sauransu, nakan yi intabiyu ga Hausawa ko kuma wadanda ke jin Hausa, don jin ta bakinsu.
Ka fara koyon harshen Hausa a kasarku, kafin ka zo kasar Hausawa. Shin lokacin da ka zo Najeriya, yaya ka ga Hausawa?
Bari in gwada maka wani misali, wannan shi ne karo na farko da na fita daga kasarmu kuma na zo nan Najeriya. Da na fito daga filin saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke nan Abuja sai na ga kamar ma na taba zuwa wannan wuri. Ka gane abin da nake nufi? Na rika ji a jikina kamar ba wannan ne karo na farko da na zo kasar nan ba, amma kuma a zahiri, shi ne zuwana na farko. Na rika jin cewa anya kuwa ban taba yin tattaki zuwa kasar nan ba? (Wannan na nufin abin da na rika karantawa, shi na rika gani a zahiri da na zo).
To, ka san Abuja shi ne babban birnin Tarayyar Najeriya, amma ba cibiyar Hausawa ba ne. Da na je Kano, na je Katsina da Sakkwato da Kebbi, na je Minna ta Jihar Neja, na ga su ne kamar kasar da Hausawa suke. Da farko dai mutanen Hausawa sun nuna mini kirki. Abu na biyu shi ne na ga kamar suna da kuzari wajen gudanar da aiki da kuma iya karbar baki. Akasarinsu sun san cewa ni ba Bahaushe ba ne, amma dai mutum ne wanda ke jin Hausa. Shi ne suka shirya mini abinci, kamar tuwon masara da su doya, miyar kuka, miyar alayyahu da shinkafa. Haka kuma da daddawa. Sai na ga cewa ban taba dandana irin wdannan abinci a China ba, amma ga shi na samu dandanonsu a nan kasar Hausa. Abin ya ba ni mamaki, kuma na ji dadinsu har wuya. Abu na uku shi ne tufafin Hausawa. Na taba sanya tufafin gargajiya, kamar na sarakuna, inda rawanin ma ake yi masa kamar kunnuwan zomo. Na sayi wannan sutura ne a kasuwar Wuse, sannan kuma ina sha’awar sanya su.
Na je wasu unguwannin Hausawa. Ka san kusan shekara daya da rabi ke nan ina aiki a nan, don haka na fara kulla zumunta tare da Hausawa da yawa. Kuma na taba yin intabiyu da Mataimakin Shugaban kasa da Ministan Babban Birnin Tarayya da wasu ministoci da yawa. Duk sun nuna mini kirki. Wannan ya zame mini abin farin ciki kuma abin alfahari, domin a gaskiya ku Hausawa kun nuna mini kirki kuma kun ba ni goyon baya kan irin aikin da nake yi. Wannan shi ya sanya ni farin ciki kuma ina godiya.
Yanzu idan ka koma kasarka ta China, da wane tunani ko tsaraba za ka tafi musu da su a matsayinka na wanda ya zauna Najeriya?
Abu na farko shi ne, Hausar da nake magana da ita ta samu gogewa, ta inganta. Wannan ita ce tsaraba ta farko saboda ina amfani da Hausa ce a wurin aiki, don haka idan na koma China zan ci gaba da gabatar da shirye-shirye da Hausa. Amma ta hanyar gudanar da aikina, Hausa za ta zama ingantatta kuma za ta goge. Wannan ita ce tsaraba ta farko. Tsaraba ta biyu ita ce, ina son in gaya wa ’yan uwana wato Sinawa ko kuma mutanen China cewa Najeriya babbar kasa ce, mai arziki kuma mai ban al’ajabi. Ba na son in ji kowace rana ana maganar bom ko wani hari ne, wannan gaskiya ne, amma ban da wannan akwai abubuwa masu kyau da yawa a Najeriya. Ina son in gaya wa ’yan uwanmu ’yan China cewa Najeriya babbar kasa ce kuma mutanenta sun nuna mini kirki, sun nuna mini karimci, inda suka karbe ni kamar wani babban bako. Ka san nan ba da jimawa ba, Firaministan kasarmu ya kammala ziyara nan kasar. Ka san muna da wata alaka ko hulda mai kyau, ba ma kawai ta fuskar tattalin arziki ko cinikayya ba ne. Muna da alaka ta fannin zirga-zirgar al’umma tsakanin kasashenmu, ta fannin wasannin motsa jiki da al’adu. Ina son in zama kamar wata gada tsakanin al’ummar Najeriya da al’ummar kasar Sin, domin inganta irin wannan dangantaka ko zumunta tsakaninmu. Wannan shi ne abin da nake son yi don bayar da gudunmowata.
Batun iyali fa?
A’a, ban yi aure ba tukunna.
Da ka zo nan Najeriya, da ka shiga kasar Hausa, ba ka hadu da wata Bahaushiya ba ka ji kana son ta?
(Ya kyalkyace da dariya sosai…). A’a, ban yi haka ba.
Daga karshe, ko kana da wani karin bayani na karkare wannan tattaunawa?
Abu na farko ita ce godiya. Godiya ga Allah, godiya gare ku saboda jaridar Aminiya da ta tattauna da ni, ina farin ciki. Da fatan Allah Ya bar zumunci tsakaninmu saboda ku takwarorinmu ne. Kai dan jarida ne kamar yadda ni ma dan jarida ne, ina son Allah Ya bar zumunci tsakanin Sashin Hausa Na Gidan rediyon China da jaridar Aminiya kuma ina fatan Allah Ya bar zumunci tsakanin China da Najeriya.