✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hattara dai iyaye

Zuwa ga Aminiya.  Gaisuwa da fatan alheri ga daukacin ma’aikatanku baki daya. Ina so a ba ni fili ne don in yi tsokaci ga iyayen…

Zuwa ga Aminiya.  Gaisuwa da fatan alheri ga daukacin ma’aikatanku baki daya. Ina so a ba ni fili ne don in yi tsokaci ga iyayen yara mata, wadanda suke barinsu su kai shekara 25 zuwa 30 ba tare da sun aurar da su ba.  A gaskiya yin haka ya saba wa ka’idar addinin Islama kuma hakan ne ke sanya matan shiga hadari a rayuwarsu.  Sannan kuma akwai wasu iyayen da ba su son aurar  da ’ya’yansu ga talaka wai sai mai mota ko kuma mai kudi komai ilimin da wanda yake son aurensu yake da shi in dai ba shi da abin duniya to shi tamkar wulakantacce ne a idonsu.
Allah Ya sa su ji kuma su gyara.
Daga Sani Shado Birnin Gwari 07058233392.
Sakonnin waya
Ga Jam’iyyar PDP
Salamun alaikum, Editan Aminiya, ga sakona game da korar Gwamnan Jihar Ribas daga PDP, wato Rotimi Amaechi, bisa zargin ya karya dokar kundin tsarin mulki jam’iyya na karba-karba a zaben 2011. Wane ne ya fara karya wannan dokar in ban da PDP? Daga Jamii Medicine Store da Isah Maiwada Malumfashi 08039515906.

Tsokaci kan dimokuradiyya
Assalamu alaikum, Edita ina so ka ba ni dma in yi Magana akan siyasar dimokuradiyyar Najeriya. Mu dai abin da za mu ce ci gaban da muka samu shi ne na fadar ’yancin albarkacin baki, amma ta bangaren harkar rayuwa, matasa ba aikin yi, ga amtsalar tsaro da tabarbarewar ilimi. Daga Jagoran Wayar wa Matasan Arewacin Najeriya Kai, Auwalu Makarkata dambatta. 08102661967.

Godiya ga Edita
Ina godiya mai tarin yawa ga Editan Aminiya. Su kuma jama’a ya kamata su san idan wnai Musulmi ya yi kuskure, nasiha ake yi ba zagi ba. Daga Misis Umar Gombe 08026504270.

Jinjina ga Aminiya
Aminiya ina yi muku jinjina. Daga Hamza Gwarzo. 07059914018.

Ta’aziyyar mutanen Baga
Editan Aminiya ina yi muku fatan alheri, ni ba ma’abociyar sauraren rediyo ba ce, amma duk kowane mako jaridarku ta Aminiya ba ta wuce ni. A nan na ga abin da ya faru a garin Baga, sai kuma na tuna wakar da mahaifina yake wa marigayi Sani Audi, inda yake cewa “ga bakon mutan Fallomi, kuma bakon mutanen Baga.” A isar mini da ta’aziyyata ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, mu ma in ta mu ta zo Allah Ya kyauta karshenmu. Daga Halima Mamman Shata Katsina. 08131014066.

Matan aure a sa sakata a baki
Edita don Allah ka ba ni dama in yi kira ga matan aure, wadanda ke shiga motar haya, su daina skain baki, suna hira da fasinjoji, kamar ba matan aure ba. Ina kira ga ’yan uwana mata su rika tunawa da ranarsu ta karshe. Daga Asma’u Khamees (Auntyn Mama) Kano 07064262851.

Bikin Dimokuradiyya
Ina taya ku murnar bikin Dimokuradiyya. Allah Ya kara taimaka mana. Allah Ya doraku ga nasara. Allah Ya karya duk makiyin Aminiya. Amin. Daga Amiru Isa Bakori 08075959086.

Fatan alheri ga Kwankwaso
Salam. Aminiya ku shigar da ni in mika godiya ga ’yan Hisba da kuma Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, bisa abin arzikin da yake yi wa talakawan Jihar Kano, musamman raya sunna ga zawarawa da ya yi. Allah Ya kara yawaita mana irin Rabi’u Musa Kwankwaso. Amin. Bissalam. Daga Isah Bishir Sabuwar kofa Katsina 08111920491.

Dokar siyasa ko ta-baci a Adamawa?
Fatan alkhairi ga Editan Amintatta. Batun dokar ta-baci da aka saka a Jihar Adamawa, anya ba siyasa a cikinsa? Daga 07045129916.

Ga Gwamna Shema
Aminiya don Allah ga sakon talakawan Jihar Katsina ga Gwamna Shema. Ba ma goyon bayan neman mataimakin shugaban kasa da kake yi. Kamata ya yi ka himmatu wajen inganta ilimi da harkokin kiwon lafiya a jiharka. Kuma amatsayinkla bna masanin dokoki, bai kamat a ace kana wasa da hankalin kananan hukumomi ba. Daga Musa Unguwar Maiyasin, danja, Jihar KAtsina 08155648155.

Kwankwaso a kara kokari
Salam Aminiya ku mika shawarata ga maigirma Kwankwaso da ya bude mana Jami’ar kur’ani ta farko a Kano, kuma ya rika zuwa ma’aikatun gwamnati da kansa ba tare da sanin Kwamishinansa ba ya kiran karamin ma’aikaci, ya tambaye shi. Shawara a kan ma’aikatar, sai sun fi ba shi shawara ta gari. Don  na je Asibitin Murtala ka yi kokari, amma don girman Allah a kara. Nagode. Daga Muhamamd Sani 08051280009.

Ga Kabiru Gaya
Editan Aminiya ka ba ni dama in yi tsokaci kan kyawawan al’adu a tsarin siyasar Alhaji Kabiru Ibrahim Gaya, musamman yadda ya kula da kusan kowace mazaba a Jihar Kano. Sai dai wani korafi mu mutanen Tiga ba mu ga hannunsa ba, musamman ganin cewa ’yan PDP sun nuna gazawa. Lallai Kabiru Gaya ka kara kaimi wajen kyautata wa al’umma. Domin idan har APC ta tabbata, tunda ’yan Najeriya na bukatar sauyi, tabbas kai za mu gabatar a matsayin jagora kuma dan takarar gwamnanmu. Allah Ya sa mu dace. Daga Ahmad Tiga 08068643446.

Za mu yi murabus daga Aminiya
Salam Edita, sama da mutum 10 za mu yi murabus da karanta Aminiya, saboda Zamfara muna korafin ba a saka sakonmu a jerin sakonni na mako. Sun fi sanya na Kanawa da Katsinawa, har wasu na ikrarin aminiya ta Katsinawa da Katsinawa ce. Ni kuma nasan Aminiya ta ’yan Najeriya ce. Ku yi adalci, kada ku rasa kwastomomi. Daga Bashir Adamu Moriki Zamfara. 07036951482.
Gwamna ya ji kiran Rimin Kebe
Rokon da al’ummar Rimin kebe suka yi ya sAmu karbuwa, domin gwamna ya amince a yi aikin. Godiya muke yi Aminiya. 07045129916.

Hattara Edita
Kalaman da jaridar Aminiya ta fitar ta ranar 3/5/2013 a shafi na 10. “dan shekara 86 ya sa saki matarsa mai shekara 79” bai dace ba, duk mutumin kirki ya jisu ba dabi’a ce ta wani bangare na kasar nan ba. Na yi tur da labarin da duk irinsa. Hattara dai Mal./Mr. Edita. Daga 08056090628.

Ga wutar rikicin PDP
Salam Aminiya, wannan wuta da ta kama PDP, Allah Ya kara rurutata. Allah Kada ka akshe wannan wuta, ta zama kamar wutar daji. Amin. Daga Adamu Suleiman  Kaugama. 08057672400.

Shawara ga Gwamnan Babban Banki
Assalamu alaikum, aminiya ga shawarata ga Sanusi Lam ido Sanusi. Ba daina buga kananan takardun kudi za a yi ba, a’a. A bugo irin na da. Daga Suleiman Musa M/fashi 08088703455.

Sulhu ko yaki?
Hankali ke gani, ba ido ba, ban taba ganin inda abokin gaba zai zare takobi ya rike a hannunsa, kuma ya ce wa abokin gabarsa wai ya zo su gaisa, kuma shi ya zo don hauka, ina kira ga gwamnati in sulhu za ta yi da ‘yan boko haram to ta janye dokar ta-baci, in kuma yaki za ta yi to ta rusa kwamitin sulhu, don ba a taba hada wuta da ruwa a kwano daya ba. Daga Yahaya Ahmed Jabo K/Hausa Jihar Jigawa.

Ga manyan PDP na Arewa
Manyan PDP kun debo ruwan dafa kanku. Ku daina kuka da Godluck, ku kuka da kanku. Daga Muhammad Kafachan 08166188009.