Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na APC, ya nemi a yi hattara da masu yada labaran karya a kan dan takarar jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu.
Wannan dai na kushe ne cikin wata sanarwa da Abdulaziz Abdulaziz, Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yada Labarai ga Tinubun ya fitar a wannan Lahadin.
- An dawo da zoben kammala makaranta bayan shekara 67 da bacewarsa
- CBN ya kara wa’adin karbar tsofaffin takardun kudi da kwana 10
A cewar Abdulaziz, “mun lura da wasu shafukan labarai na bogi musamman a Facebook suna yada wani labarin karya da yarfe irin na siyasa wanda suke rawaito cewa wai an kama wasu motoci da kudade mallakin dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC.
“Wannan magana karya ce tsagwaronta wadda makiya suka shirya domin domin bata sunan Alhaji Ahmed Bola Tinubu.
“Abin lura a nan shi ne babu wata madogara da su wadannan masu yada labarun karya suka dogara da ita wajen rawaito wannan magana ta bogi.
“Muna jan hankali mutane da su lura da cewa a kwanakin da suka rage mana kafin shiga zabe, ’yan siyasa marasa tsoron Allah da dama za su yi ta kokarin yada labaran karya da sharri domin bata sunan abokan hamayyar su da suke ganin cewa ba za su iya kayar da da su a akwatin zabe ba sai sun hada da karya da sharri domin bata musu suna.
Abdulaziz ya ci gaba da cewa, “dan takarar jam’iyyar APC, Jabagan Borgu ya sha fadar cewa shi bai yarda da yin sharri ko yarfen siyasa ba domin ba sahihiyar hanya ce ta cin zabe ba.
“Abinda muka dogara da shi shi ne a bar mutane su yi zabin dan takarar da suka ga ya dace kuma yana da kwarewar aiki da zai iya kawo wa kasa ci gaba, ba tare da an bi haramtaciyyar hanya ba wajen rudar da tunanin masu zabe.
“Muna kira ga jama’a da su yi watsi da wannan labarin bogi marar hujja wanda wasu makiya kuma marasa son zaman lafiya zuka kirkira,” a cewar Abdulaziz.