✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota: ’Yan wasan kungiyar Wikki Tourist sun tsallake rijiya da baya

Hatsarin dai ya faru ne a kan hanyar dajin Kibo dake kusa da birnin Jos na jihar Filato a ranar Alhamis.

’Yan Wasan Ajin Kwararru na Kungiyar kwallon kafa ta jihar Bauchi, Wikki Tourist sun tsallake rijiya da baya sakamakon wani hatsarin mota da ya kai ga konewar motar da suke ciki kurmus.

Hatsarin dai ya faru ne a kan hanyar dajin Kibo dake kusa da birnin Jos na jihar Filato a ranar Alhamis.

’Yan wasan dai na kan hanyarsu ne ta zuwa Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom domin fafata wasa da kungiyar Dakkada FC dake jihar lokacin da suka hadu da iftila’in.

Rahotanni sun ce ’yan wasan dai sun bar masaukinsu ne a Bauchi da misalin karfe 4:30 na Asuba, yayin da hatsarin kuma ya faru da misalin 7:00 saura ’yan mintuna na safiyar Alhamis a kusa da Jos.

Sai dai ba a sami asarar rai ko da guda daya ba sakamakon hatsarin, in banda ta kayayyaki da suka hada da jakunkuna da wayoyin salula na ’yan wasan da shugabannin kungiyar.

A cewar daya daga cikin ’yan wasan wanda yake cikin motar mai suna Damala Ezekiel, tayoyin motar biyu ne suka fashe sannan kuma motar ta akama da wuta.

Damala ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Lamarin ya faru ne da safe a Hawan Kibo muna kan hanyarmu ta zuwa Akwa Ibom domin karawa da Dakkada ranar Lahadi.

“Daga nan ne kuma motar ta kama da wuta. Mun gode Allah da ya tserar da mu, babu asarar rai ko daya, babu kuma wanda ya ji rauni, mun gode Allah,” inji shi.

Idan dai za a iya tunawa, shekaru 11 da suka gabata sai da wasu ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Jimeta dake Yola su 15 da mai horar da su suka gamu da ajalinsu bayan motar su ta yi hatsari.