Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), ta tabbatar da mutuwar mutane biyu, sannan biyar sun ji rauni a wani hadarin mota da ya ritsa da su a kauyen Dakatsalle da ke kan hanyar Kano zuwa Zariya.
Kwamandan Hukumar reshen Jihar Kano, Mista Zubairu Mato ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
- An kwaso ’yan Najeriya 255 da suka makale a Saudiyya
- Ya kamata a dauki matasa 50m aikin soji —Tinubu
- Buhari ya taya Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwa
- ‘Yadda na gudu a hannun masu garkuwar da suka kama mu’
“Mun samu kiran neman agajin gaggawa da misalin karfe 3:15 na dare a ranar 29 ga Maris, 2021.
“Bayan samun kiran ne nan take muka aike da jami’anmu kuma suka isa wurin da hadarin ya auku don ceto mutane da misalin 3:40 na dare”, a cewar Mato.
“Hadarin ya ritsa da mutane maza 13 kuma daga ciki biyu sun rasa rayukansu, sannan wasu biyar sun jikkata,” a cewarsa.
Kwamandan, ya ce hadarin ya auku ne sakamakon gudun wuce kima tsakanin wata motar haya kirar Peugot 306 mai lamba TFA 429 da tirela mai lamba KTJ 574 XA.
Mato ya kara da cewa an garzaya da wanda suka samu raunuka zuwa babban asibitin garin Kura inda kuma aka mika gawawwakin wadanda suka rasu ga ‘yan uwansu.