Wani hatsarin mota da ya auku a kauyen Sabuwar Miya a Karamar Hukumar Ganjuwa a Jihar Bauchi ya yi sanadin mutuwar mutum shida.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ne, a Bauchi, Yusuf Abdullahi ya sanar sa hakan ga NAN a ranar Lahadi.
- Kirsimeti: Fafaroma ya yi kira da a gaggauta kawo karshen yakin Ukraine
- Fitattun ’yan Najeriya 10 da suka rasu a 2022
“Hatsarin ya rutsa da mutum 22 da ke cikin motar.
“Mutum shida sun rasa rayukansu nan take bayan faruwar hatsarin.”
Kwamandan ya kara da cewa mutum 16 kuma sun ji rauni a sanadin hatsarin.
Ya ce hatsarin ya samu wata mota ce kirar bas Toyota Hiace mai lamba BA124 AO6.
Kwamandan ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon rashin kyawun tayar motar.
Abdullahi, ya ce wadanda suka ji rauni an kai su Babban Asibitin Kafin Madaki, inda ake ba su kulawar da suke bukata.
Amma ya ce an shirya don mayar da wasu da suka samu munanan raunuka zuwa Asibitin Koyarwa na Tafawa Balewa don kula da su.
Ya bukaci masu tuka ababen hawa da suke tabbatar da lafiyar abun hawansu kafin yin tafiya.