✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 15 a Kogi

Hatsarin mota ya yi ajalin akalla mutum 15 a garin Koton-Karfe da ke Karamar Hukumar Lokoja ta Jihar Kogi. Hukumar Kiyaye Hadura ta Najeriya (FRSC)…

Hatsarin mota ya yi ajalin akalla mutum 15 a garin Koton-Karfe da ke Karamar Hukumar Lokoja ta Jihar Kogi.

Hukumar Kiyaye Hadura ta Najeriya (FRSC) ce ta tabbatar da mutuwar mutanen da wasu mutum biyar kuma da suka samu munanan raunuka a hatsarin da ya auku.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa hatsarin ya auku ne bayan da wata motar fasinja kirar J-5 da wata tankar mai suka yi taho mu gama a kan babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja da safiyar ranar Talata.

Babban Kwamandan FRSC mai lura da jihar Stephen Dawulung, ya ce tuni aka kai wadanda suka samu raunukan asibiti domin ba su kulawar gaggawa.

Mista Dawulung ya ce saba dokokin hanya da direban motar fasinjan ya yi ne ya haddasa aukuwar hatsarin.