✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 12 a Kano

Gadar ta karye sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka ranar Juma'a.

Mutum 12 sun rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin mota da ya auku a kan titin Doguwa da ke Karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano.

Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), ta ce hatsarin ya auku ne sakamakon karyewar gadar Shiburu da ke garin Riruwai na karamar hukumar.

  1. Mutum 145 ne za su shirya auren Yusuf Buhari da ’yar Sarkin Bichi
  2. Gani ya Kori Ji: Babbar Sallah, harbo jirgin soji

A cewar Kwamandan hukumar Zubairu Mato, hatsarin ya faru a ranar Juma’a sakamakon karyewar gadar ta dalilin mamakon ruwan sama da ya rika sauka a kwanakin baya bayan nan.

Ya ce mota kirar Sharon mai launin tsanwa ta fada cikin ruwa wanda a dalilin haka mutum 12 suka mutu da dama suka ji rauni.

Bayanai sun ce biyar daga cikin fasinjojin da suka riga mu gida gaskiya, ‘yan gida daya da ke kan hanyarsu ta zuwa Karamar Hukumar Dambatta a jihar.

Wani wanda ya ganewa idonsa faruwa hatsarin, ya shaida wa Aminiya cewar, gadar ta karye ne sakamakon mamakon ruwan sama, kuma babu wanda ya lura da gadar ta karye sai bayan faruwar hatsarin.