Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) a ranar Litinin ta ce akalla ’yan Najeriya 2,233 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota a watanni hudun farko na 2021.
Shugaban hukumar na kasa, Boboye Oyeyemi ne ya bayyana hakan yayin wani taro da aka gudanar ta bidiyo mai suna ‘GabFest’ na Babatunde Fashola karo na biyar mai taken ‘Sauka lafiya: Gina al’umma mai kiyaye dokokin tuki’.
- ’Yar Najeriya ta haifi ’yan 6 bayan shekara 6 da haihuwar tagwaye
- 2023: Manyan abubuwa 7 da za su iya tarwatsa APC a Kano
Ya ce an sami mace-macen ne a cikin hadurra 4,459 da suka ritsa da mutum 28,828.
A cewarsa, alkaluman na tsakanin watan Janairu zuwa Afrilu sun nuna cewa mutum 691 sun mutu a watan Janairu, 497 a Fabrairu, sai 480 a Maris, yayin da 565 suka mutu a watan Afrilu.
Boboye wanda ya bayyana gudun wuce sa’a a matsayin babban ummul-aba’isun hadurra a Najeriya ya kuma ce rubabbun motoci da bai kamata su hau tituna ba suma suna taka gagarumar rawa.
“An sami yawan masu amfani da hanya a kan tituna, dalilin kenan da yasa aka sami yawan hadurran a watannin Janairu da Afrilu. Yawan wadannan hadurran da yawan mace-macen da ake samu a cikinsu gaskiya ya fara wuce iyaka.
“Rashin shingayen duba direbobi ma na taka muhimmiyar rawa. Idan da muna da irin wadannan shingayen, za mu rika zakulowa tare da tantance masu gudun wuce sa’a,” inji shi.