Hatsarin mota ya lakume rayukan akalla mutum 43 daga ranar Lahadi zuwa Litinin a jihohin Osun, Yobe, Legas, Delta da Akwa Ibom.
Akalla mutum 20 ne suka mutu ta hatsarin mota a Jihar Osun, inda wata tankar gas ta fadi a kan babban titin Ilesa zuwa Akure.
- Hatsarin mota ya salwantar da rayukan fiye da mutum 20 a Osun
- ’Yan sanda bakwai sun mutu a hatsarin mota
Wani ganau ya ce, “tankar ta fadi a kan hanya, gas ya kwarara kuma ta haifar da cunkoso daga bisani wuta ta tashi ta kuma kona motocin da ke wurin.
“Mutane da dama ciki har da kananan yara da motoci akalla guda takwas ne suka kone.
“Ban san adadin mutanen suka kone ba, wasu sun zama toka an kuma kai da yawa asibiti”.
Wasu shaidu sun ce sun hangi gawarkwaki akalla guda 20 kwance a kasa, wasu ma sun zama toka.
Kakakin Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Osun, SP Yemisi Opalola, ta ce motar ta kama da wuta tare da kone motoci takwas.
Sai dai ta ce ba za su iya tantance adadin mutanen da suka mutu ba amma an kai wadanda suka samu rauni asibitoci don yi musu magani.
Karon bus da babbar mota a Yobe
A Jihar Yobe, Kwamandan FRSC, Yelwa Dio, ya tabbatar mana cewa mutum 17 sun rasu sakamakon hatsarin mota, wasu hudu kuma sun samu raunuka a kauyen Zubali da ke kan hanya Potiskum zuwa Kano.
Ya ce hatsarin ya faru ne daren Lahadi, yayin da wata bus ta yi karo da babbar mota.
“Jam’ianmu sun fitar da gawar mutum 17 a cikin motocin biyu, maza 14 da mata uku, duk sun mutu.
“Mun kai gawarwakin Babban Asibiti Potiskum, wadanda suka rauni kuma na karba magani a asibitin”, inji Duo.
Ya daganta hatsarin da mugun gudu da kuma rashin bin dokar tuki.
“Ya kamata direba ya tabbatar fitilar motarsa tana da haske kuma fasinja su rika kwabar direban da ke mugun gudu saboda idan aka yi hatsarin dukkansu zai shafa”, inji shi.
‘Tsohuwa ta haddasa hatsari a Delta’
A Jihar Delta, hatsari kan hanyar Ughelli-Warri ya yi sanadiyar mutuwar mutum biyu, wasu shidda kuma suka samu raunuka.
Wani ganau ya ce wata mota kirar Toyota Hiace ta yi hatsari a lokacin da direbanta ya yi kokarin kauce wa wata tsohuwa a daura da babban cocin Zion Covenant Bible Church.
Fashewar taya ta ci mutum biyu a Legas
An rasa mutum biyu a hatsarin motar da ya auku a gadar Third Mainland da ke Legas.
Wani shaida ya ce hatsarin ya auke ne sakamakon fashewar tayar motar da mutanen ke ciki.
Ya ce direban motar da wani mutum da ba iya tamtancewa ba sun rasu a nan take, sauran fasinjojin kuma sun samu rauni.
Mutum biyu sun mutu a Akwa Ibom
A Akwa Ibom kuwa, FRSC ta tabbatar cewar mutum biyu sun mutu a hatarin mota biyu da suka auku a wurare daban-daban.