Mutum hudu aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da rutsa da su a Kauyen Wailo da ke Karamar Huku,ar Darazo ta Jihar Bauchi.
Shugaban Hukumar KIyaye Hadurra ta Kasa reshen Jihar, Yusuf Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zantawarsa da Aminiya a ranar Juma’a.
- Sabon Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya ya kama aiki
- An kama barawo mai shigar Fatalwa a garin Gutu
A cewarsa, hatsarin ya auku ne da misalin karfe 2.45 na ranar Alhamis a kan babban hanyar Bauchi zuwa Maiduguri.
Ya ce gudun wuce gona da iri ne ya yi sanadiyar aukuwar hatsarin wanda ya rutsa da maza hudu da tuni an killace gawarwakinsu a babban Asibitin garin Darazo.
“Hatsarin ya rutsa da wata motar fasinja kirar Toyota mai lamba BEN256TA da kuma wata motar kirar Golf mai lamba MUB739QW.
“Bayan mun amsa kiran neman agajin gaggawa, nan da nan muka tura jami’anmu zuwa wurin da lamarin ya faru domin aikin ceto.
“Jami’anmu sun garzaya da duk wadanda hatsarin ya rutsa da su zuwa Babban Asibitin Darazo, inda a nan ne likitoci suka tabbatar da mutuwar hudu daga cikinsu,” inji Abdullahi.
Ya kara da cewa, a halin yanzu wadanda suka jikkata na ci gaba da samun kulawa a Asibitin na Darazo.
Ya gargadi matafiya da masu ababen hawa a kan gudun wuce kima da su rika kiyaye dokokin hanya da mahukunta suka shar’anta domin kauce wa tsautsayi na asarar rayuka da dukiya.