✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya kashe mutum 15 a Afirka ta Kudu

Mutum 37 sun jikkata a sakamakon hatsarin da ya auku a Tshwane.

Akalla mutum 15 ne suka kwanta dama sakamakon mummunan hatsarin mota da ya auku tsakanin wata babbar motar daukar kaya da wata bas a yankin Patryshoek da ke Arewacin Tshwane a Afirka ta Kudu.

Kakakin Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa a Tshwane, Thabo Charles Mabaso, shi ne ya bayyana hakan.

Mabaso ya ce, hatsarin ya auku ne da safiyar Juma’a inda motocin da abin ya shafa suka yi taho-mu-gama.

“Jami’an ba da agajin gaggawa sun hallara wurin da hatsarin ya faru inda suka tarar da mutane zube a kasa, wasu kuma makale a cikin motocin,” inji Mabaso.

Ya ce, mutm 15 daga ciki nan take suka ce ga garinku nan, yayin da aka kwashi wasu mutum 37 da suka ji raunuka zuwa asibitoci daban-daban don kula da su.

Ya zuwa hada wannan rahoto, jami’in ya ce hukumoin na ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin.

(NAN)