Akalla mutum 16 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babbar hanyar Funtua zuwa Gusau.
Aminiya ta ruwaito cewa, hatsarin ya auku ne a tsakanin motoci hudu bayan da kan wata motar daukar kaya ya kwace kuma ta gwabza wa wasu kananan motoci uku a kusa da Fegin Dan Marke mai makwabtaka da birnin Gusau.
Bayan babbar motar ta daukan kaya, sauran jerin motocin da hatsarin ya ritsa da su a sakamakon gudun da ya wuce ka’ida sun hadar da wata Peugeot Wagon, Golf Saloon, da Golf Wagon.
Hatsarin ya auku ne ranar Laraba jim kadan bayan wucewar Gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle a hanyarsa ta komawa Gusau daga Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Samun rahoton wannan mummunan lamari tun kafin ya isa fadarsa, ya sanya Gwamnan ya dawowa wurin cikin gaggawa, inda ya bada umarnin a garzaya da gawarwakin zuwa Asibitin Yariman Bakura da ke Gusau.
A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Alhaji Zailani Bappah, ya fitar, ya ce Gwamnan ya jajantawa ’yan uwan wadanda suka rasun tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.
Jami’in Hulda da Al’umma na Hukumar Kiyaye Hadurra reshen Jihar Zamfara, Yassar Shehu, ya tabbatar wa da wakilanmu wannan lamari.