Daruruwan ababen hawa sun shiga cikin mawuyacin hali a kan hanyar Kaduna-Abuja bayan wata babbar mota makare da tarkacen kayan karafa ta yi hatsari a dab da sansanin Alheri Camp, da ke kan hanyar.
Hatsarin da ya faru kusan kilo mita 35 daga garin Kaduna a safiyar ranar Talata ya sa motoci tafiyar hawainiya na kilomitoci masu yawan gaske.
- Matasan Arewa na goyon bayan mulki ya koma yankin Yarabawa a 2023
- Coronavirus ta kashe Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Akwa Ibom
- ‘Barayin mutane sun haukace bayan an yi musu dukan kawo wuka’
Shaidu sun ce motar da ta yi hatsarin ta toshe hannu daya na titin, wanda hakan ya jefa daruruwan matafiya cikin halin kaka-ni-ka-yi.
Wani da abin ya faru a kan idonsa ya ce rashin kyan hanyar na taimakawa wurin haddasa munanan hadura a babbar hanyar.
Ya ce, hatsarin ya haifar da cunkoson ababen hawa da suka yi jerin gwano suna tafiya da kyar har zuwa Rijana.
Jami’an Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) sun ci wuya a yayin da suke aikin kawar da cunkoson, saboda gajen hakurin wasu masu ababan hawa.
Titin Kaduna zuwa Abuja babbar hanya ce da a baya-bayan nan ’yan bindiga suka addabe ta da kai hare-haren satar matafiya don karbar kudin fansa.