✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota: Mata 11 sun kone kurmus a hanyar Zariya zuwa Kano

Hatsarin ya auku ne a Marabar Gwanda, dab da shiga Zariya

Wani mummunar hatsarin mota da ya auku a garin Marabar Gwanda da ke dab da shiga Zariya a hanyar Zariyan zuwa Kano ya yi sanadiyar konewar mata 11 kurmus.

Bayanai sun nuna cewa cewa dukkan mutanen da suka rasu a hatsarin mata ne, kuma ya faru ne da yammacin ranar Asabar, tsakanin wata mota kirar Hilux da wata mai kirar bas.

Malam Abdul’aziz Isiyaku, mazaunin unguwar Tudun Jukun da ke Zariya, mahaifi ne ga yara biyu daga cikin mutanen da suka kone a hatsarin ya ce, “Dukkan wadanda suka kone mata ne kuma akwai ’ya’yana biyu; Zainab Abdul’aziz mai shekara 16 da kuma Aisha Abdul’aziz mai shekara takwas.”

Ya ce a lokacin da suka isa wajen, sun iske motar na ci da wuta.

A cewar Malam Abdul’azizi, bayanai sun nuna motar Hilux din ce ta je ta doki bas din tana tsaka da tafiya, inda nan take ta fadi kuma ta kama da wuta.

Sai dai ya ce direba da yaron motar suna Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Shika, inda suke samun kulawa.

Duk kokarin jin ta bakin Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Zariya ya ci tura saboda mai magana da yawunsu ya ce ba ya gari bai san yadda lamarin ya faru ba.

To sai dai mazauna kauyen sun ce ita motar Hilux din ce take gudun wuce sa’a yayin da take kokarin kwace wa sai direbanta ya hango wata motar da ke zuwa sai ya dawo  da baya ya bigi motar fasinja da ke kan hanyar, inda ya kara mata gudu ta kife ta kama da wuta.

Sun ce mutane sun yi iya kokarinsu wajen cire sauran fasinjoji ciki har suka kone amma suka gaza yin hakan har mutanen suka kone.

Hatsarin na ranar Asabar dai daya ne daga cikin da dama da ake yawan samu a wannan hanyar.

Ko a baya-bayan nan, wasu motocin tare da wata tankar mai sun yi taho-mu-gama kuma sun kone mutane masu yawa da ransu.