Ana fargabar cewa wani kwale-kwale ya nutse da wasu mutum bakwai a yankin Otuan da Ayama na Karamar Hukumar Ijaw ta Kudu da ke Jihar Bayelsa.
Daga cikin wadanda nutsewar jirgin ruwan ta yi ajalinsu har da wata mata mai juna biyu da kuma wata mace mai yi wa kasa hidima.
- Dakaru sun kashe gomman mayakan ISWAP a gabar Tafkin Chadi
- Rasha ta hana ’yan jaridar Birtaniya 29 shiga kasarta
Aminiya ta ruwaito cewa, hatsarin wanda ya faru ranar Asabar da rana, ya kuma yi ajalin wata uwa da ’ya’yanta biyu da kuma wata dattijuwa mai kimanin shekaru 70 a duniya.
Rahotanni sun ce kwale-kwalen mai daukar fasinjoji 15, ya daki wani shinge ne a cikin ruwa wanda a dalilin haka ya nutse yayin da yake tunkarar garin Ayama domin komawa gabar ruwa a daidai lokacin da ake tafka ruwan sama.
Kawo yanzu dai ana ci gaba da laluben gawawwakin ragowar fasinjojin da suka nutse a hatsarin kwale-kwale, inda gwanayen linkaye ke ci gaba da kai komo wajen aikin ceto.
A cewar Shugaban Kungiyar Sufurin Kwale-Kwale, Joseph Shedrack, tuni aka tsare direban kwale-kwalen, Lucky Christopher saboda zarginsa da tukin ganganci.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce suna jiran karin bayani kan bayanan mutanen da lamarin ya rutsa da su.