✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin jirgin ruwan Neja: An gano gawar mutum 9

An gano gawar mutanen ne kwanaki hudu bayan aukuwar hatsarin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja ta ce an gano gawarwakin mutum bakwai da wani hatsarin kwalekwale ya rutsa da su a Karamar Hukumar Shiroro ta jihar kwanaki hudu bayan faruwar lamarin.

Shugaban sashen yada labarai da ayyuka na musamman na hukumar, Ibrahim Audu, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce duk wadanda aka gano gawarwakinsu sun ’yan kauyen Zangoro ne, amma har yanzu ba a gano sunayen biyu daga cikin wadanda suka mutu ba.

Sunayensu sun hada da Farida Muntari, Sharhabila Sagir, Abubakar Sadiq, Na’ima Ibrahim, Amina, Safaratu Ibrahim, Sadiq Ibrahim da Rafiya Yakubu, dukkansu daga kauyen Zangoro.

Aminiya ta ruwaito cewa wani jirgin ruwa dauke da mutum 34 ya kife da yammacin ranar Alhamis, inda mutum 10 suka mutu, yayin da aka ceto mutum 24.

Fasinjojin wadanda akasari ’yan kasuwa ne, sun hada da maza 20 da mata 14, daga cikin su akwai yara mata takwas da manya mata shida.

Sauran sun hada da yara maza guda biyu da maza manya guda 18.

A baya-bayan nan an samu yawaitar hatsarin jirgin ruwa, musamman a jihohin Taraba, Sakkwato, Kebbi da sauransu.