✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hatsarin babbar mota ya lakume rayuka 2 a Anambra

Akalla mutum biyu sun mutu a wani hatsari da ya rutsa da wata babbar mota da karama a kan babbar hanyar Enugu zuwa Onitsha a…

Akalla mutum biyu sun mutu a wani hatsari da ya rutsa da wata babbar mota da karama a kan babbar hanyar Enugu zuwa Onitsha a daren ranar Litinin.

Kwamandan shiyya na Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) a jihar Anambra, Andrew Kumapayi ya bayyana haka a birnin Awka na jihar ranar Talata.

Andrew ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 11 na dare, sakamakon tare hanyar da wata karamar mota ta yi bayan ta lalace ba tare da ta yi amfani da alamar hatsari ta “C” domin ankarar da masu tahowa ba.

Ya ce hatsarin ya rutsa da mutum biyar, yayin da biyu daga cikinsu suka mutu a nan take.

“Hatsarin ya rutsa da wata koriyar A-Kori-Kura. Rahotanni dai sun tabbatar mana da cewa, wata motar haya ce ta yi gyara kuma direbanta bai yi amfani da alamar hatsari ta “C” ba.

“To sai dai babbar motar ta afka wa karama ta danne mutanen ciki da kuma kashe kwandastanta da kuma wani fasinja lokacin da suke tsaka da tura ta.

“Ragowar mutane biyun da ke cikin motar su ma sun samu raunuka, kuma nan take jami’an hukumarmu da hadin gwiwar ‘yan sanda suka garzaya da su asibitin Toronto da ke Onitsha”, inji jami’in.

Daga nan sai ya shawarci masu amfani da ababen hawa su tabbatar suna amfani da alamar nuna akwai hatsari a gaba ta “C” idan suna gyaran motocinsu a kan hanya domin ankarar da masu tafiya.

Kwamandan ya ce, “Muna shawartar masu tuki kan su kasance suna da wannan alamar akalla guda biyu, ta yadda za a ajiye daya daga kimanin nisan mita 100 daga wurin hatsarin.

“Sannan na biyun kuma sai a ajiye shi akalla mita 50 daga motar,” inji shi.