Kimanin mutum biyar ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya auku a kan titin Kwanar Dumawa zuwa Kunya da ke Karamar Hukumar Minjibir a Jihar Kano.
Hatsarin wanda kuma ya yi sanadiyar jikkatar wasu mutum biyu ya faru ne sakamakon taho mu gama tsakanin wata mota kirar Golf da babur mai kafa uku da aka fi sani da Adaidata Sahu.
- An tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Imo
- PSG za ta raba gari da Ramos, Tottenham za ta dauki Conte
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Kano, Zubairu Mato, ya ce hatsarin ya afku ne a sakamakon gudun wuce kima da direbobi ke yi.
Ya ce bayan faruwar lamarin ne aka sanar da jami’ansu da misalin karfe 1:05 na rana ranar Talata.
“Cikin gaggawa jamianmu suka isa wurin inda suka garzaya da wadanda abin ya ritsa da su zuwa Babban Asibitin Minjibir da Danbatta wanda a nan likita ya tabbatar da mutuwar biyar daga cikinsu,” a cewar Mato.
Kazalika, Mista Mato ya sanar da wakilinmu cewa da hudu daga cikin wadanda suka rasu maza ne sai kuma mace guda daya, a yayin da sauran mutum biyu da suka ji rauni duka maza ne.
Idan dai ba a manta ba ko a makon da ya gabata irin wannan hatsarin ya afku a Kanon inda dalibai biyar na Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi suka rasa rayuwarsu, tare da jikkatar wasu da dama.