✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hassana Hunkuyi: Tun daga makarantar firamare na fara rubutu

Malama Hassana Abdullahi Hunkuyi na daya daga cikin marubutan Hausa da tauraruwarsu ke haskawa. Yaushe ta fara rubutu, me ya sa take rubutu, littattafai nawa…

Malama Hassana Abdullahi Hunkuyi na daya daga cikin marubutan Hausa da tauraruwarsu ke haskawa. Yaushe ta fara rubutu, me ya sa take rubutu, littattafai nawa ta rubuta? Wadannan da ma wasu tambayoyin da suka shafi Adabin Hausa da ma al’amuran yau da kullum, marubuciyar ta amsa su a tattaunawarta da Aminiya 

Ko za ki bayyana mana tarihinki a takaice?

Sunana Hassana Abdullahi, mata ga Isah Buhari Yusuf. An haife ni a garin Hunkuyi, Jihar Kaduna. Na fara karatun firamare a Kaduna daga baya na karashe a Central Primary School Hunkuyi. Da na gama na tafi makarantar sakandaren ’yan mata ta kwana da ke Kaduna, watau GGSS Kawo Kaduna.
Bayan nan sai na yi aure a nan Hunkuyi, daga nan kuma na ci gaba da karatun takardar shaidar NCE, ta hanyar karatu daga gida, wato DLS. Bayan nan, na yi ta fafutukar komawa karo ilmi har sau hudu amma Allah bai sa na samu gurbi a jami’a ba amma bana in sha Allahu ina sa ran zan sami gurbin karo karatun.
Game da aiki kuwa, a yanzu haka ina koyarwa a nan Hunkuyi, inda nake rike da wani bangare na Model Primary School a matsayin shugaba, wato Head Teacher. Ina kuma taka sana’ar sayar da atamfa, shadda, kayan yara da yadiddika.
Tun yaushe kika fara rubutu, wadanne irin littattafai kike rubutawa kuma me ya ja ra’ayinki har kika fara rubutu?
Zan iya cewa na fara rubutu tun a 1995 amma littafin bai shiga kasuwa ba sai a 2005. Ina yin rubutu ne a kan zamantakewar al ‘umma.
Abin da ya ja ra’ayina har na fada harkar rubutu shi ne, sha’awa; domin tun ina makarantar firamare nake dan rubuta tatsuniyoyi. Wannan sha’awar ta ci gaba da yaukaka har na je sakandare. Ko da na gama karatun sakandare sai na ji ni ma ina son ba da gudunmawata don bunkasa harshen Hausa.
Wane littafi ne kika fara rubutuwa, wanne ya fara shiga kasuwa kuma ya zuwa yanzu littattafai nawa kika wallafa kuma suka shiga kasuwa?
Littafin da na fara rubutawa shi ne, Makircin Zuciya kuma shi ne littafina da ya fara shiga kasuwa. Ya zuwa yanzu na yi littattafai goma sha bakwai, sha biyar sun shiga kasuwa.
Ko kina cikin kungiyoyin marubuta? Wadanne ne kuma ko kin gamsu da yadda kungiyoyin suke tafiyar da harkokinsu na bunkasa Adabin Hausa?
Ina cikin kungiyoyi guda uku, su ne: Mace Mutum, LardinZazzau da Alkalam Kaduna. Na gamsu dari bisa dari da yadda kungiyoyin ke tafiyar da harkokinsu na bunkasa adabi.
Ko an taba karrama ki dangane da rubuce-rubucen da kike yi?
kungiyarmu ta Alkalam ta taba karrama ni bisa gagarumar gudunmawar da nake ba da wa wajen bunkasa Adabin Hausa.
A wane lokaci ko yanayi kika fi jin dadin yin rubutu?
Na fi jin dadin yin rubutu da yamma, bayan Sallar La’asar da kuma bayan Sallar Subahi.
A matsayinki na marubuciya ko wane abu kika samu ko kike samu da kike farin ciki da shi?
Jama’a rahama ne. Ni kam na same su ko in ce ina kan samun su, domin kusan kullum sai na yi sabbin makarantan littattafaina; wadanda suke mini addu’o’in da ke kara mini kwarin gwiwa.
Wane buri kike da shi dangane da harkar rubutu a nan gaba?
Burina a harkar rubutu a nan gaba shi ne, sakon da muke isarwa ya shiga lungu da sako, ta yadda harshen Hausa da al’adun Hausawa za su kewaye kasar nan da ma makwabtan kasarmu. Ina burin ganin Adabin Hausa ya bunkasa, ya shahara, ya zama gagarabadau a duniya.
Ko kina da shawarwari ga gwamnati, al’umma da kuma makaranta littattafanki?
Shawarar da zan ba gwamnati ita ce, ta hada tafiya da marubuta. Ta hakan ne sakonninta za su isa ga al’umma cikin takaitaccen lokaci. Gwamnati ta shigo cikin harkar, kamar yadda ta shiga ake tafiya tare da ita a sauran kafafen yada labaru don yada manufofinta.
Shawarata ga al’umma ita ce, mu zauna lafiya da juna, mu kaunaci juna, mu mutunta juna, mu daina zalunci, mu yi wa shuwagabanninmu biyayya.
Masu karatun littattafaina kuwa, shawarata a gare su ita ce, don Allah su daina wulakanta littattafanmu, domin akwai sunan Allah a ciki. Sannan idan lokacin Sallah ya yi, a rika aje karatun littafin, ba ma littafin Hausa kadai ba, kowane irin abu kuke yi, a aje, a je a yi Sallah. Mata kada ku yarda karatun Hausa ya shagaltar da ku daga hidimta wa maigida da yara ko baki. ’Yan mata a kula da taimakon iyaye, ka da a bar su da aiki.
Shawara ta karshe ita ce, ku yi aiki da abubuwan kwarai da kuka karanta a littattafanmu, ku yi fatali da marasa amfani. Kowane dan Adam ajizi ne, don haka makaranta ku yi mana uzuri idan mun yi kuskure!
Ga shi marubuta na shirin gudanar da gagarumin bikin ranar marubutan Hausa ta duniya, mene ne ra’ayinki game da wannan biki?
A ganina, wannan gangamin taro zai dada zaburar da tsoffin marubutan da suka je hutun dindindin. Bikin zai kara kaimi ga marubutan da ake damawa da su a yanzu. Yayin da gangamin taron zai kara wa sabbin marubuta kwarin gwiwar zage damtse wajen wasa alkalumansu don daukaka Adabin Hausa da al’adun Hausawa. Hakika na hango da izinin Allah marubuta za su kai wani kololuwar matsayin da kowa zai yi mamaki. Gangamin taron marubuta na duniya zai kara tagomashin da zai dawo da tsoffin makaranta ruwa, za kuma a yi gagarumar nasarar kara samun yawaitar sabbin makaranta fiye da shudaddun lokuta.