✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harsashin bindiga ya cizge ’ya’yan marainan wani saurayi a Edo

Al’ummar Ayen a Karamar Hukumar Uhunwode da ke Jihar Edo, sun tsinci kawunansu cikin firgici yayin da harsashin wata bindiga kirar gida ya tsige ’ya’yan…

Al’ummar Ayen a Karamar Hukumar Uhunwode da ke Jihar Edo, sun tsinci kawunansu cikin firgici yayin da harsashin wata bindiga kirar gida ya tsige ’ya’yan marainan wani saurayi mai shekara 17 a karshen makon da ya gabata.

Aminiya ta samu cewa saurayin ya boye bindigar ne a cikin wandonsa inda tsautsayi ya sanya ta tashi yana tsaka da tafiya, lamarin da ya sanya ya ce ga garinku nan take tun kafin a kai masa dauki.

Kazalika, wakilinmu ya samu cewa babu wanda ke da masaniyar musabbabin tashin bindigar a yayin da saurayin mai suna Osaro ya kasance a ware da mutane a yayin da lamarin ya auku.

Wannan lamari ya janyo dimuwa saboda aukuwarsa a lokacin da ake faman rikici tsakanin al’ummar Ayen da kuma makwabtansu na Owegie kan mallakar wasu gonaki.

Yayin da aka tuntubi Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Edo, SP Chidi Nwanbuzor domin jin ta bakinsa, ya ce bashi da wata masaniya a kan lamarin.

A kwanan nan ne aka yi wata mummunar arangama tsakanin matasan al’ummomin biyu a yayin da suka yi karan batta da juna.